Ya debo ruwan dafa kansa: An tsinci gawar wata Soja a dakin saurayinta

Ya debo ruwan dafa kansa: An tsinci gawar wata Soja a dakin saurayinta

Wata sabuwar Soja a rundunar Sojan kasan Najeriya, Patience Amos Yau ta mutu a dakin saurayinta dake unguwar Damilu, cikin garin Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa na jahar Adamawa.

Jaridar Guardina ta ruwaito Soja Patience yar shekara 23 ta rasu ne bayan wani rikici daya auku tsakaninta da saurayinta Ali Muhammad Wakil, wanda yake ikirarin shi ma jami’in Soja ne, kuma yana aiki da asibitin Sojojina 68 dake Yaba jahar Legas.

KU KARANTA: Wata gawurtacciyar yar fashi ta shiga komar jami’an Yansandan Najeriya

Rahotanni sun bayyana alamu sun nuna Patience ta mutu tun a ranar 12 ga watan Janairu, amma sai Ali ya boye gawarta a cikin dakinsa, har sai a ranar Litinin jama’a suka farga bayan warin gawara ya dumama unguwar.

Makwabtansu sun ce sun ji muryar Patience da Ali daga dakin Ali yayin da suke cacar baki, amma basu san me ya faru daga wannan lokaci ba, amma sai suka fara zargin akwai matsala bayan kwashe kwanaki 3 basu sake ganin budurwar ba.

“Abin da ya fi damunmu shi ne warin da muka dinga ji yana fitowa daga dakin, sa’annan kuma ga shi kuma an kulle kofar dakin ta waje, wannan yasa muka kara tabbatar da cewa akwai matsala, don haka muka karya tagar dakin, a haka muka gano gawarta har ya fara rubewa.” Inji wani makwabcinsu.

Nan da nan jama’an suka sanar da mai unguwa, wanda ya kai kara ga ofishin Yansanda, inda su kuma suka nemi mahaifin Patience. Mahaifinta, Amos Yau ya bayyana cewa shi dai ya san yarinyarsa ta tafi yin kitso ne, amma daga nan bata sake komawa gida ba.

Amma da suka kira wayarta da yamma, sai tace tana kan hanyar komawa gida, zuwa ranar Lahadi da suka sake kiran wayar sai suka ji ta a kashe, daga nan basu sake jin duiyarta ba har sai bayan kwanaki 4 da aka shaida musu labarin mutuwarta.

Daga karshe kaakakin Yansandan jahar Adamawa, Sulaiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace sun kama Muhammad Wakil, kuma a yanzu haka suna gudanar da bincike a kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel