Dalilin da ya sa ta’adanci zai cigaba a arewa maso gabas – Ndume

Dalilin da ya sa ta’adanci zai cigaba a arewa maso gabas – Ndume

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Ali Ndume, ya ce matsalar ta’addanci zai ci gaba a arewa maso gabas saboda rashin isassun kayayyaki da sojoji.

Yan ta’addan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare kan garuruwa a yankin arewa maso gabas, inda hakan ya sa dubban mutane barin gidajensu.

Lamarin ta’addanci ya fi munana ne a jihohin Borno da Adamawa.

Da yake zantawa da jaridar Punch a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, Ndume ya ce ta’addanci zai ci gaba har sai idan gwamnatin tarayya ta tura isassun kayayyaki da kuma kara yawan sojoji a yankin.

Ndume ya ce mutane da dama sun zama marasa galihu, sannan cewa yan farar hula a garuruwan da lamarin ya faru sun tsere daga yankunan.

Amma ya kara da cewa gwamnati na kokari don tabbatar da komawar mutane gidajensu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe Shugaban PDP a Delta

Sanatan ya koka a kan sace Lawan Andimi, Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) A karamar hukumar Micika da ke Adamawa wanda Boko Haram suka yi a ranar Alhamis.

Ya bukaci sojoji da su yi duk abunda ya dace don tabbatar da cewar an sake shi da kuma dawo da zaman lafiya ga garuruwa da jihohin da lamarin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel