Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da zaben Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da zaben Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

- Kotun koli ta tabbatar da zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa a ranar Talata, 21 ga watan Janairu

- Kotun ta kuma yi watsi da karar da ke kalubalantar zaben Fintiri

- Ta riki hukuncin kotun zaben gwamnan jihar da na kotun daukaka kara wadanda suka tabbatar da Fintiri

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa kotun koli ta tabbatar da zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa a ranar Talata, 21 ga watan Janairu.

Hakazalika da take zartar da hukunci karkashin jagoranci Justis Dattijo Mohammed, kotun ta yi watsi da karar da ke kalubalantar zaben Fintiri.

Kotun ta riki hukuncin kotun zaben gwamnan jihar da na kotun daukaka kara wadanda suka tabbatar da Fintiri a matsayin sahihin zababben gwamnan Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Da karfe 2 na rana Kotun koli za ta yanke hukunci kan zabukan gwamnan Adamawa da Benue

A wani labari makamancin wannan mun ji cewa kotun ta tabbatar da zaben Samuel Ortom a matsayin gwamnan jihar Benue.

Babbar kotun, da take zartar da hukunci ta kwamitinta na alkalai bakwai karkashin jagorancin Justis Olabode Rhodes-Vivour, ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, Emmanuel Jime ya daukaka kan nasarar gwamna Ortom na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel