Adamawa: Boko Haram sun sace Shugaban CAN a Garin Michika

Adamawa: Boko Haram sun sace Shugaban CAN a Garin Michika

Ana zargin cewa ‘Yan Boko Haram sun dauke Rabaren Lawal Andimi, wanda shi ne shugaban kungiyar CAN a Garin Michika a jihar Adamawa.

Jairdar Daily Trust ta rahoto cewa an daurawa Sojojin kungiyar ta’addan laifin sace shugaban kungiyar addinin ne bayan wani hari da aka kai.

A Ranar Alhamis da ta gabata, 2 ga Watan Junairu, 2019, ‘Yan Boko Haram su ka kai hari, har su ka sace babban Faston da ke Kauyen na Michika.

Hakimin Michika, Ngida Kwace, shi ne ya bayyanawa Mai girma Mataimakin gwamna, Crowther Seth, wannan a lokacin da ya kawo masu ziyara.

Mista Crowther Seth ya ziyarci Garin Michika ne a jiya Ranar Asabar, bayan samun labarin ta’adin da ‘Yan Boko Haram su ka yi a wannan Yankin.

KU KARANTA: An ji labarin mutuwar babban Jami’in gwamnati a wani hadarin gas

Adamawa: Boko Haram sun sace Shugaban CAN a Garin Michika

'Yan ta'adda sun dauke Shugaban Kiristoci na CAN a Jihar Adamawa
Source: Twitter

“An dauke Faston ne lokacin da Boko Haram su ka kawo mana hari. Ba a sake ganinsa ba tun bayan da ‘Yan ta’addan su ka jefa shi cikin mota.”

“Tun daga wannan lokaci, ba mu sake jin labarinsa ba, ko kuma daga bakin wadanda su ka sace shi.” Inji Mai martaba watau Ngida Kwache.

Hakimin Michika, Kwache, ya ce a cikin wata mota kirar Toyota Hilux wadannan ‘Yan ta’adda da ake tunanin Boko Haram ne, su ka jefa Faston.

Hakiman Yankin Michika, Gulak, da Koppa sun dade su na rokon a karo masu jami’an tsaro. Seth, ya sanar da su cewa gwamnati za ta tashi tsaye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel