Abin da ya sa mu ka fice daga PDP, mu ka kafa R-PDP a Adamawa - Umar Ardo
Rahotanni sun ce wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Adamawa, sun balle daga uwar jam’iyya, sun kafa Taware da su ka kira ‘Reformed PDP’ ko kuma ace R-PDP.
Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Litinin 26 ga Watan Nuwamban 2019, daya daga cikin jagororin jam’iyyar, Dr. Umar Ardo, shi ya bada wannan sanarwa na ballewa daga PDP.
Umar Ardo ya yi wannan jawabi ne a gaban Manema labarai a Ranar Litinin dinnan ya na mai cewa ba za su cigaba da biyewa saba dokar da aka dade ana yi a cikin jam’iyyar PDP ba.
Ardo ya ke cewa ya kamata kwamitin shugabannin rikon-kwarya na jihar su sauka su shirya zabe domin a nada ainihin shugabannin jam’iyya a Adamawa, wanda ya gagari kwamitin.
Jigon ya shaidawa ‘yan jarida cewa: “Maganar ita ce duk wani ‘dan kwamitin rikon kwarya da zai yi takarar shugaban jam’iyya, sai ya ajiye mukaminsa. Amma ba haka aka yi a Adamawa ba.”
KU KARANTA: Kashi 80% na APC daga Jam’iyyar PDP su ka fito – Sule Lamido
Dr. Ardo ya cigaba da kokawa: “Shugabannin rikon-kwaryan ne gaban dayansu su 11, su ka zauna a cikin otel a Yola, su ka rikidar da kansu, su ka zama ainihin shugabannin jam’iyya na jiha.”
Babban ‘dan siyasar ya ce ya na jagorantar R-PDP ne bayan duk kokarin da ya yi na ganin an yi gyara ya ci tura. Ardo yace ya rubuta takarda ga Uwar jam’iyya amma ba a dauki mataki ba.
Shugaban PDP na jihar, Shehu Tahir, ya maida martani ya ce Umar Ardo ya yi takarar zaben fitar da gwanin gwamna a karkashin shugabannin da ya ke ikirarin cewa ba na yanka bane.
Ko ma dai ya lamarin ya ke, shugaban PDP na Adamawa ya bayyana cewa tuni Ardo ya tashi daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP don haka bai da damar tserewa har ya kafa kungiya a cikinta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng