Yan bindiga sun bindige wani babban limamin Coci har lahira a jahar Adamawa

Yan bindiga sun bindige wani babban limamin Coci har lahira a jahar Adamawa

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da hari a gidan wani babban limamin coci Rabaran Denis Bagauri, wanda ake yi ma inkiya da Fasto Nyako, inda suka bindige shi har lahira.

Daily Trust ta ruwaito a daren Lahadi, 19 ga watan Janairu ne yan bindigan suka bi Fasto Denis har zuwa gidansa dake kauyen Nasarawo Jereng, a cikin karamar hukumar Mayo Belwa na jahar Adamawa ne, a can suka karar da rayuwarsa.

KU KARANTA: Lamari ya ta’azzara: Duk wanda suka zalunce mu Allah Ya tsine musu albarka – Kwankwaso

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce Fasto Denis ya taba zama hadimi ga tsohon gwamnan jahar Adamawa, Murtala Nyako, haka zalika ya taba zama mashawarci ga tsohon gwamnan jahar, Bindow Jibrilla a kan harkokin addini.

Majiyar ta bayyana cewa da fari yan bindigan sun yi kokarin kai hari a gidan wani babban sakatare ne, amma sai suka hangi tarin mafarauta a kofar gidan, don haka suka yi mi’ara koma baya suka zarce gidan Fasto Denis.

Fasto Denis yana aiki ne da cocin Lutheran Church of Christ, LCCN, a kauyen Nassarawo Jereng. Ko da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar Adamawa, sai kaakakinta, Sulaiman Nguroje ya tabbatar da harin, kuma yace sun fara bincike game da harin.

A wani labarin kuma, Anyi musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram da kuma mayakan ISWAP dake karkashin jagorancin kungiyar ta’addanci ta duniya, watau ISIS a kan wasu mata 13 da kowanne bangare yake so.

Wannan musayar wuta da aka yi a sansanin ISWAP dake kauyen Sunnawa cikin yankin Abadam a kusa da iyakar kasar Nijar yayi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda da dama daga bangarorin biyu, tare da jikkata wasu da kuma lalata motocin yaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel