Abun Bakin Ciki
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya sanar da hana hawan sallah da duk wasu shagulgula domin zaman makoki da alhinin mutanen da suka mutu a ambaliyar Mokwa.
Wani shugaban al'umma ya naushi Sarki mai masaukin baƙi a wurin taron da gwamna ya kaddamar da aikin titi, lamarin ya faru ne daga an ce mutum ya canza wuri.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya daga jihar Plateau mai suna Hajiya Jamila Muhammad da ta je aikin hajji a Saudiyya a ranar Litinin.
Oniroko na Irokoland, Sunmaila Olasunkanmi Abioye Opeola ya riga mu gidan gaskiya, masarauta ta ce za a yi masa jana'iza yau Asabar a jihar Oyo da ke Kudu.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya mika sakon jaje ga al'ummar Mokwa da ke jihar Neja bisa ambaliyar ruwan da ta afku a yankin da ke jihar Neja.
Sarkin Epe da ke jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya, Shefiu Ọlatunji Adewale ya kwanta dama yana da shekara 86, za a yi janazarsa yau Asabar.
Rahotanni daga jihar Neja sun tabbatar da cewa tawagar masu aiki ceto sun tsamo gawarwakin mutane 115 zuwa ƙarfe 5 na yammacin jiya Juma'a a Mokwa.
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya bayyana cewa ɗan sandan da ke gadin mahaifiyarsa ne ya harbi ƴar uwarsa, Atsi Kefas a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Jalingo.
'Yan daba sun kai hari tashar saukar jirgi da ke cikin kamfanin siminti na Ashaka da ke a Gombe. Jami'in NSCDC ya samu nasarar kashe ɗaya daga cikin 'yan daban.
Abun Bakin Ciki
Samu kari