Bola Tinubu
Matan da za su zama ministoci a gwamnatin Bola Tinubu sun hada da Dr. Suwaiba Said Ahmad. Su ne sababbin matan da suka shiga gwamnatin APC mai mulki.
Akwai wasu lokutan da Sanatan Boro ta Kudu, Ali Muhammadu Ndume ya cire kara, ya soki Bola Tinubu duk da Sanata Ali Ndume ya na cikin jagorori a jam’iyyar APC.
Sanata Mohammed Ali Ndume ya bayyana cewa garambawul din da Bola Tinubu ya yi ci gaba ne da ake bukata amma har yanzu akwai sauran aiki a gabansa.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen da ake yi a Najeriya kan neman mulkin soja ta tabbata inda ta ce ba a ganin kokarin da gwamnatin ke yi.
Tsohuwar Ministar mata a gwamnatin Bola Tinubu, Uju Kennedy-Ohanenye ta nuna goyon bayanta wurin taya shugaban inganta Najeriya inda ta ce tana tare da shi.
Al'ummar Najeriya da dama sun yi ta korafi bayan ganin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a cikin masallacin Juma'a na Abuja da Bola Tinubu.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaban kasa yana da niyya mai kyau ga ƴan Najeriya, ya bukaci a ci gaba da yi masa addu'a.
Tushen wutar lantarkin Najeriya ya lalace sau 105 a mulkin Buhari da Bola Tinubu. Tun fara mukin Buhari aka samu lalacewar tushen wutar lantarki sau 93 a Najeriya.
IMF ya ce babu ruwansa a cire tallafin fetur a Najeriya. Daraktan Afrika na asusun, Abebe Selassie ne ya fadi haka, ya ce amma mataki ne mai kyawun gaske.
Bola Tinubu
Samu kari