Yan ta'adda
Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na ta bayyana rashin jin dadin yadda masu lalata kayan gwamnati ke jawo wa kasa asara, inda aka kashe N8.8bn domin gyara.
Yan sanda sun kama yan daba da aka fi sani da ƴan sara suka a jihar Bauchi. An kama yan sara suka 16 dauke da makamai masu haɗari, za a kaisu kotu bayan bincike.
Dakarun sojoji na rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a jihar Borno. Sojojin sun kuma kwato makamai masu tarin yawa.
Wani magidanci ya koka yayin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da 'ya'yansa hudu ciki har da yaro dan shekara biyu a Kaduna.
Rundunar sojin Najeriya ta saki wuta kan yan ta'addar Boko Haram a jihar Borno.Jirgin sojojin sama ya saki boma bomai kan tarin yan ta'addar Boko Haram.
Yan sanda sun kama matasa biyu da suka zaune a gari bisa taimakon yan bindiga masu garkuwa da mutane a daji a karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya koka kan ayyukan masu ba 'yan ta'adda kayan aiki da bayanai. Ya ce suna kawo babban cikas.
Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya Bianca Ojukwu ta ce Bola Tinubu zai saki Nnamdi Kanu. Ministar ta ce sakin Kanu zai taimaka wajen kawo zaman lafiya.
Matashiya yar TikTok a jihar Sokoto, Hamdiyya Sidi Shareef ta fadi abubuwan da suka faru da ita bayan fitar da wani bidiyo da ake zargin ta ci mutuncin gwamna.
Yan ta'adda
Samu kari