Yan ta'adda
Ayyukan yan ta'adda ya yi kamari a yankin Arewacin kasar nan, inda aka aka sace mutane akalla 7568 a cikin shekara daya kawai, lamarin da ya sa aka fara ramawa.
An ruwaito cewa 'yan daba sun farmaki rukunin gidajen M.I Wushishi da ke Minna, babban birnin jihar Neja inda suka ba mazauna unguwar umarnin ficewa daga gidajensu.
Janar Halliru Akilu, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya ya nemi gwamnatin Bola Tinubu da ta yi amfani da tsarin IBB wajen magance rashin tsaro
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce ba gaskiya ba ne zargin da ake yi na cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna wariya a rabon mukamai da ya yi.
A wannan labarin za ku ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu masu garkuwa da mutane guda biyu da aka yi nasarar cafkewa a Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta dauki alhakin harin da aka kai kauyen jihar Yobe wanda ya yi sanadin kisan kimanin mutane 87.
Tsohon dan sanda ya fallasa dalilin gaza kama yan bindiga masu amfani da wayar tarho domin kira a kawo musu kudin fansa. Ya ce yan siyasa ne suka jawo lamarin.
A wannan rahoton za ku ji cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sake tafka rashin imani inda su ka kashe matashin mai shekaru 19, Anas Zubairu bayan karbar N17m.
Mataimakin gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana zai jagoranci jami’an gwamnati zuwa jana’izar mutanen 37 da 'yan ta'adda suka kashe a Yobe. Sojoji suka kwaso gawarwakin.
Yan ta'adda
Samu kari