Yaki da rashawa a Najeriya
Yayin da ake ci gaba da binciken tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, babban ɗansa, Abdul'aziz Ganduje ya ziyarci ofishin yaki da cin hanci a jihar.
Mai shari’a Emeka Nwite na babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ya amince da bukatar hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) na kama Yahaya Bello.
Wanda ake kara na 6 ne kawai ta hannun lauyansa, Nureini Jimoh, ya gurfana a gaban kotun yayin da Ganduje da sauran wadanda ake karar 7 ba su halarta ba.
Rahotanni na nuni da cewa wasu jami'an hukumar da ke yaki da cin hanci da rasha (EFCC) dauke da makamai sun mamaye gidan Yahaya Bello da ke birnin tarayya Abuja.
Matashin lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya ce za’a sha tiri-tiri a wannan shari'ar Abdullahi Ganduje da gwamnatin Kano. Kuma kama Ganduje abune mai matukar wahala.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta sake shigar da sabbin tuhume-tuhume kan Abdullahi Ganduje da suka shafi karkakatar da kudi.
Bashir Ahmed, tsohon hadimin tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai yiwuwar abin da ya faru da Adam Oshiohmole ne zai faru da Ganduje.
Jam’iyyar APC gundumar Ganduje ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Ganduje a kan zargin bada cin hancin da gwamnatin Kano ke yi masa.
Za a gurfanar da Ganduje da wasu shida gaban kotun a ranar Laraba mai zuwa bisa tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci da rashawa, abin da ya jawo dar dar a Kano.
Yaki da rashawa a Najeriya
Samu kari