Tuhumar Rashawa: Jam’iyyar APC Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Abdullahi Ganduje

Tuhumar Rashawa: Jam’iyyar APC Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Abdullahi Ganduje

  • Jam'iyyar All Progressives Congress ta sanar da cewa ta dakatar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar na kasa
  • Mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a Halliru Gwanzo ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu
  • Jam'iyyar reshen gundumar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa ta dakatar da Ganduje ne a kan zargin cin hancin da ake yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Jam’iyyar All Progressives Congress reshen gundumar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

APC ta dauki mataki kan zargin rashawar da ake yi wa Ganduje
APC ta ce girman zargin da gwamnatin Kano ke yi wa Ganduje ya sa aka dakatar da shi. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Halliru Gwanzo ne ya sanar da dakatarwar da yake zantawa da manema labarai a jihar Kano ranar Litinin.

Kara karanta wannan

"An yi hawan Sallah da shi": Masarautar Zazzau ta yi babban rashi, Hakimin Ikara ya rasu

" Dalilin dakatar da Ganduje" - APC

Gwanzo ya bayar da danganta zargin bada cin hancin da gwamnatin jihar Kano ke yi wa Ganduje a matsayin dalilin dakatarwar, jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun yanke shawarar dakatar da Dr. Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar saboda girman zargin da ake yi masa."

- In ji Gwanzo.

A halin da ake ciki, kokarin jin ta bakin babban sakataren yada labarai na shugaban jam’iyyar APC na kasa, Mista Edwin Olufo, ya ci tura saboda an kasa samun wayarsa.

Za a gurfanar da Ganduje a Kotu

Legit Hausa ta ruwaito maku cewa ranar Laraba mai zuwa ne babbar kotun Kano ta tsayar domin fara sauraron karar da gwamnatin Kano ta shigar kan Abdullahi Ganduje da wasu shida.

Gwamnatin Kano na zargin Ganduje, mai dakinsa Farfesa Hafsat Umar da wasu mutane biyar da laifuffukan da suka shafi karkatar da kudi.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rasa rai yayin da miyagu suka farmaki ɗan takarar gwamna

Sai dai tun bayan da Ganduje ya samu sammacin ya yi martani tare da zargin Gwamna Asbba Kabir Yusuf da lullube gazawarsa a mulkin jihar ta hanyar dauko da batun bincikarsa.

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike

Tun da fari, Legit ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir ya kafa wasu kwamitoci guda biyu da zasu gudanar da bincike kan yadda Abdullahu Umar Ganduje ya mulki jihar Kano.

Kwamitin farko zai duba badakalar kudi da karkatar da kadarorin jihar da ake zargin Ganduje da iyalansa sun yi a lokacin da yake kan mulkin jihar.

Kwamiti na biyu kuma zai binciki irin ta'asar da aka yi a lokacin zabubbukan jihar daga 2015 zuwa 2023 musamman kan rahoton satar yara da kuma kashe mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel