Tuhumar Rashawa: Shari’ar Gwamnatin Kano da Abdullahi Ganduje Ta Gamu da Cikas

Tuhumar Rashawa: Shari’ar Gwamnatin Kano da Abdullahi Ganduje Ta Gamu da Cikas

  • Gwamnatin jihar ta gaza gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa, dansa da wasu mutane
  • Lauyan gwamnati, Barka Y. A. Adamu, ya shaida wa kotun cewa ba su iya mika takardar tuhuma ga wadanda ake kara ba
  • An ruwaito cewa wanda ake kara na shida ne kawai ta hannun lauyansa, Nureini Jimoh, ya gurfana a gaban kotun a zaman na yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta gaza gabatar da takardar tuhumar laifuffuka ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa, dansa da wasu biyar.

Gwamnatin Kano ta gaza gurfanar da Ganduje da iyalansa a gaban kotu
Ganduje, matarsa da dansa da wasu biyar ba su halarci zaman kotun Kano ba. Hoto: @OfficialAPCNg, @Kyusufabba
Asali: Facebook

Wannan gaza cika sharudan da gwamnatin jihar ta yi ya jawo cikas ga kudurinta na gurfanar da wadanda take zargin gaban wata babbar kotun jihar a yau Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin rijiyoyin mai kan rashin biyan haraji

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an shirya gurfanar da Ganduje da sauran a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume takwas da suka hada da cin hanci da rashawa da karkatar da kudade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje bai halarci zaman kotu ba

Baya ga Ganduje da iyalansa, sauran wadanda ke cikin karar sun hada da Jibrilla Muhammad, sai kamfanonin Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.

Gwamnatin jihar Kano a karar da ta shigar kan wadanda ake tuhumar ta ce ta tattara shaidu 15 don ba da shaida a kansu.

A zaman na yau a gaban mai shari’a Usman Mallam Na’abba, wanda ake kara na 6 ne kawai ta hannun lauyansa, Nureini Jimoh, ya gurfana a gaban kotun yayin da wanda ake kara na 1, 2, 3, 4, 5, 7 da 8 ba su halarta ba.

Kara karanta wannan

Kano: Babban lauya ya fadi abin da zai iya faruwa a shari'ar Ganduje

Lauyan gwamnati ya nemi alfarmar kotu

Lauyan gwamnatin jihar Kano, Barka Y. A. Adamu, ya shaida wa kotun cewa ba su iya mika takardar tuhumar ga wadanda ake kara ba, jaridar Independent ta ruwaito.

Adamu, ya roki kotun da ta bada izinin mika takardar tuhumar ga wadanda ake karar ta wata hanya daban amma lauyan wanda ake kara na 6 yaki yarda da hakan.

Jimoh ya bukaci masu gabatar da kara da su "yi aikinsu yadda ya kamata", tare da yin nuni da cewa babu wani hurumin shari'a kan wannan bukatar.

An dage sauraron karar har zuwa ranar 29 ga Afrilu, 2024.

"Ina nan daram" - Ganduje ga Abba

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya aika sako ga gwamnatin jihar Kano kan shugabancin jam'iyyar APC.

Ganduje ya shaidawa Gwamna Abba Yusuf cewa har yanzu shine shugaban APC na kasa kuma yana nan "daram dam" a kan kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel