Badakalar N84bn: Kotu Ta Amince da Bukatar Hukumar EFCC Na Cafke Yahaya Bello

Badakalar N84bn: Kotu Ta Amince da Bukatar Hukumar EFCC Na Cafke Yahaya Bello

  • Rahotan da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) ta samu izinin kama Yahaya Bello
  • Mai shari’a Emeka Nwite na babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ya ba EFCC takardar izinin kamun a yammacin yau Laraba, 17 ga Afrilu
  • Wanan na zuwa ne duk da wata babbar kotun jihar Kogi ta haramtawa EFCC kama tsohon gwamnan na Kogi ko tsare shi ko kuma gurfanar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta amince da bukatar hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) na kama Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Babbar kotun ta yanke hukunci kan yunƙurin EFCC na cafke tsohon gwamnan Kogi

Babbar Kotun Tarayya Abuja ta ba hukumar EFCC izinin kama Yahaya Bello
An ba hukumar EFCC takardar izinin kama Yahaya Bello Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Facebook

Kotun ta ba EFCC izinin cafke tsohon gwamnan jihar na Kogi, a shirye-shiryen gurfanar da shi a ranar Alhamis, talabijin na Channels ya ruwaito.

Kotun Kogi ta hana kama Yahaya Bello

Mai shari’a Emeka Nwite ya baiwa hukumar EFCC takardar izinin kamun nan take a yammacin yau Laraba, 17 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne bayan wata babbar kotun jihar Kogi ta yanke hukuncin hana EFCC kama tsohon gwamnan ko tsare shi ko kuma gurfanar da shi gaban kuliya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kotun da ke zamanta a Lokoja, ta hana EFCC tauye hakkin dan Adam a kan tsohon Gwamna Yahaya Bello.

EFCC ta mamaye gidan Yahaya Bello

Tun da fari, mun ruwaito cewa jami'an hukumar EFCC dauke da makamai sun mamaye gidan Yahaya Bello da ke unguwar Wuse shiyya ta 4 a Abuja.

Kara karanta wannan

EFCC: An yi ta harbe-harbe yayin da Gwamnan Kogi ya sulale da Yahaya Bello

Jami'an sun tare dukkanin hanyoyin da za su kai ga zuwa gidan tsohon gwamnan jihar na Kogi, a wani abu da Yahaya Bello ya kira "yunkurin kama shi da karfin tsiya."

Wannan ba zai rasa nasaba da zargin karkatar da akalla Naira biliyan 84 da hukumar ke yi wa tsohon gwamnan ba, da wasu tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci da rashawa.

Gwamnan Kogi ya dura gidan Yahaya Bello

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto yadda gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ya dura gidan mai gidansa, Yahaya Bello.

An yi zargin cewa Ododo ya kai wa tsohon gwamnan Kogi dauki ne domin kare shi daga jami'an hukumar EFCC da ke yunkurin kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel