Kano: Babban Lauya Ya Fadi Abin da Zai Iya Faruwa a Shari’ar Ganduje

Kano: Babban Lauya Ya Fadi Abin da Zai Iya Faruwa a Shari’ar Ganduje

  • Abba Hikima, wani matashin lauya daga jihar Kano ya ce yana ji a jikinsa ba lallai ne Ganduje ya gurfana gaban kotun da kansa ba
  • Hikima ya yi nuni da cewa gwamnatin Kano ta gurfanar da Ganduje gaban kotu ba tare da bin wasu matakai na shari'a ba
  • Lauyan ya ce kama Ganduje abune mai matukar wahala idan gwamnatin Kano bata samu goyon bayan gwamnatin tarayya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Wani lauya daga Kano, Abba Hikima ya magantu kan batun gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da ake shirin yi a yau Laraba, 17 ga Afrilu.

Abba Hikima ya magantu kan shari'ar Ganduje da gwamnatin Kano
Babban lauyan ya ce kama Ganduje zai zama abu mai matukar wahala ga gwamnatin Kano. Hoto: @Kyusufabba, @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Abba Hikima ya ce yana ji a jikinsa ba lallai ne Abdullahi Ganduje ya gurfana gaban kotun da kansa ba, kuma kama shi zai yi wa gwamnatin Kano matukar wahala.

Kara karanta wannan

Ana shirin gurfana gaban kotu, Ganduje ya aika muhimmin sako ga gwamnatin Kano

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, Hikima ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shigar da wannan karar ba tare da bin wasu matakan shari'a ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Matakan gurfanar da mai laifi" - Hikima

Hikima ya ce:

"A al'adance, ana fara shari'ar aikata laifuffuka a Najeriya ta hanyar masu shigar da kara su nemi izinin kotu domin kama wanda ake zargi ko kuma ta hanyar aika masa da takardar sammaci.
"A wannan gabar ne masu shigar da kara ke yi wa wanda ake zargin tambayoyi da kuma tattara dukkanin shaidu a kan tuhumarsa.
"Daga nan sai kuma lauyoyi su shirya abin da suke kira ‘shirya gabatar da tuhume-tuhume’ wanda a karshe ya kai ga an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya."

- Abba Hikima

Me zai faru idan ba a bi matakan ba?

Kara karanta wannan

Lauya a Kano ya fadi abin da ya kamata Ganduje ya yi, ya magantu kan zargin Gwamnati

Amma lauyan ya ce rashin bin wannan matakai yana buɗe kofa ga waɗanda ake tuhuma su iya kawo nakasu ga shari'arsu ta hanyoyin doka marasa iyaka.

Za su iya guje wa karbar takardar sammacin masu laifi da za a iya kiran su a basu, ko kuma su kawo tsaiko ga takardar ba da izinin kamasu da zarar an gansu.
"Ko ma su iya kalubalantar hurumin kotun da aka shigar da su karar a gabanta kafin a gurfanar da su a gabanta."

- A cewar lauyan.

Abin da zai iya faruwa da Ganduje

Matashin lauyan ya ce gwamnatin Kano ta yanke hukunci na yin komai gaba-gadi ta hanyar shigar da kara ba tare da an bi matakan gurfanar da wanda ake tuhuma ba.

"Ganduje ba wai tsohon gwamnan kawai bane, shi ne shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa wanda yake yawo da dimbin jami’an tsaro da suka shirya kare shi ko ta halin kaka.

Kara karanta wannan

Kano: Muhuyi Magaji ya yi magana kan fara binciken Gwamna Abba, ya taɓo Ganduje

"A takaice za’a sha tiri-tiri a wannan sharia. Kuma kama Ganduje ma abune mai matukar wahala idan gwamnatin Kano bata samu goyon bayan gwamnatin tarayya ba."

- A cewar Abba Hikima.

Ganduje zai gurfana gaban kotu

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa yau Laraba ne babbar kotu a Kano ta tsaida a matsayin ranar da za ta fara sauraron karar da aka shigar da Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnatin Kano ta gurfanar da Ganduje a gaban kotun ne bisa zarginsa da aikata almundahana da shida matarsa da wasu biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel