Zargin Cin N84bn: EFCC Ta Dura Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Abuja

Zargin Cin N84bn: EFCC Ta Dura Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Abuja

  • Rahotanni da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa jami'an hukumar da ke yaki da cin hanci da rasha sun mamaye gidan Yahaya Bello
  • Jami'an sun yi wa gidan tsohon gwamnan jihar Kogi kawanya, wanda ke a unguwar Wuse shiyya ta 4 a babban birnin tarayya Abuja
  • Har zuwa yanzu babu taka-mai-man dalilin wannan mamayar, amma dai EFCC na tuhumar Yahaya Bello da karkatar da Naira biliyan 84

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ke unguwar Wuse shiyya ta 4 a babban birnin tarayya Abuja.

Jami'an hukumar EFCC sun mamaye gidan Yahaya Bello dake Abuja
Mamaye gidan Yahaya Bello na zuwa kwanaki kadan bayan ganawarsa da Bola Tinubu. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

Hotunan da jaridar SaharaReporters ta gani a ranar Laraba sun nuna wasu jami’an hukumar dauke da makamai sun yi wa gidan tsohon gwamnan kawanya.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya shiga sabuwar matsala yayin da majalisar Kaduna ta kafa kwamitin bincike

An ruwaito cewa hukumar ta mamaye gidan ne kwanaki kadan bayan da tsohon gwamnan ya yi wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu, a fadar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

N84bn: EFCC na tuhumar Yahaya Bello

Jaridar The Punch ta rahoto cewa har yanzu ba a iya tabbatar da dalilin mamaye gidan Yahaya Bello ba.

Kakakin hukumar EFCC na kasa watau, Dele Oyewale, bai amsa kiran waya ba.

Sai dai jaridar Tribune Online ta gano cewa jami’an sun hana shige da fice a titin da ke kaiwa zuwa gidan tsohon gwamnan na Kogi.

Sai dai a baya EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello, da dan uwansa Ali, da wani Dauda Sulaiman, da kuma Abdulsalam Hudu a gaban mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

EFCC ta gurfanar da Yahaya a gaban kotun a watan Maris na 2024 bisa zargin karkatar da kudi har Naira biliyan N84, kamar yadda hukumar ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsoffin gwamnoni 4 da sanatocin Arewa 8 a Majalisa da ba su gabatar da kudiri ba a watanni 10

Yahaya Bello ya zargi EFCC da bata suna

Hukumar a cikin tuhume-tuhume 17 da ta yi wa kwaskwarima, ta zargi Bello da karkatar da kudade, cin amana, da almubazzaranci da kudade har N84,062,406,089.88.

Da take mayar da martani kan lamarin, ofishin yada labarai na tsohon gwamnan, a cikin wata sanarwa, ya yi tir da abin da jami'an suka yi, yayin da ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya ja kunnen EFCC.

Ofishin yada labaran ya kara da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar na shirya makarkashiya domin bata sunan Yahaya Bello da cin zarafinsa ta hanyar zarge-zarge.

Gwamnatin Kogi ta kare Yahaya Bello

A wani labarin, Legit ta rahoto gwamnatin jihar Kogi ta fito ta yi martani kan tuhumar da hukumar EFCC ke yi wa tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar ya fitar, ya zargi EFCC da ƙoƙarin ɓata sunan Yahaya Bello ta hanyar zarginsa da karkatar da kudaden jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel