Ganduje: Hukumar PCACC Ta Kaddamar da Sabbin Tuhume Tuhume a Kan Tsohon Gwamnan Kano

Ganduje: Hukumar PCACC Ta Kaddamar da Sabbin Tuhume Tuhume a Kan Tsohon Gwamnan Kano

  • Muhuyi Magaji, shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar Kano ya ce sun gabatar da sabbin tuhume-tuhume a kan Abdullahi Umar Ganduje
  • Magaji ya ce tuhume-tuhumen da hukumar ta gabatar somin tabi ne kawai kan irin binciken badakalar da aka tafka a gwamnatin Ganduje
  • Daga cikin laifuffukan da hukumar ke zargin Ganduje ya aikata akwai karkatar da N51.3bn na kananan hukumomi zuwa asusun wasu mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen jama’a ta jihar Kano ta ce ta sake shigar da sabbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

Hukumar PCACC ta shigar da sabbin tuhume-tuhumen rashawa kan Ganduje
Daga tuhume-tuhumen da ake yi wa Ganduje akwai karkatar da kudin kananan hukumomi. Hoto: @OfficialAPCNg, @MuhuyiMagaji
Asali: Twitter

Zarge-zargen da hukumar ta PCACC ta shigar kan Ganduje sun shafi almundahana da kuma yin amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya dokar ta baci da umarnin harbe 'yan daba a Arewacin Najeriya

"Abin da ke faruwa a yanzu somin tabi ne," in ji shugaban hukumar, Muhuyi Magaji, a cikin shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Ganduje

Muhuyi Magaji ya ce:

“Yanzu haka muna gabatar da kara kan wata badakala ta karkatar da N51.3bn na kananan hukumomi daga asusun gwamnati zuwa asusun wasu mutane, kuma mun gano mutanen.”

Magaji ya yi zargin cewa gwamnatin Ganduje ta kwashe Naira biliyan 1 daga asusun jihar ana saura wata daya wa’adin gwamnatinsa ta kare a watan Mayun 2023.

Ya yi zargin cewa an aike da kudin ne ga wasu 'yan canjin kudi ba tare da an yi amfani da kudin wajen gyaran hanya kamar yadda aka ce ba.

“Muna da shari'a kan badakalar N4bn da aka fitar daga asusun ajiyar kudin shiga na jihar Kano zuwa wani kamfanin noma. Yanzu haka wadannan tuhume-tuhumen na gaban kotu."

Kara karanta wannan

Al'ummar Kano sun nuna fargaba kan yadda shari'ar Ganduje zata kawo rikici a jihar

- Muhuyi Magaji.

Shugaban hukumar PCACC na Kano ya dage kan cewa hukumar na da hurumin bincike kan zargin almundahana da laifuffukan da gwamnatin Ganduje ta yi.

Ganduje zai gurfana gaban kotu

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa a gobe Laraba, 17 ga watan Afrilu ne tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje zai gurfana gaban babbar kotun jihar.

Gwamnatin jihar ce ta gurfanar da Ganduje da iyalinsa da wasu bisa zargin karkatar da makudan kudade a lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel