Badakalar $720, 000: Yadda Muka Yi da Tsohon Gwamna Yahaya Bello Inji Shugaban EFCC

Badakalar $720, 000: Yadda Muka Yi da Tsohon Gwamna Yahaya Bello Inji Shugaban EFCC

  • Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana yadda Yahaya Bello ya nuna ya fi karfin amsa gayyatar ta
  • A cewar hukumar ta ba shi duk wata dama da zai tattauna da ita cikin mutunci amma ya ki mutunta damar.
  • Shugaban hukumar ne ya bayyana haka yayin da ya ke labarta yadda suka yi da tsohon gwamnan ta wayar tarho kafin fara yunkurin kama shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana yadda Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi, ya watsa musu kasa a ido.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya dauki $720,000 ya biya kudin makarantar yaronshi a waje, Shugaban EFCC

EFCC and Yahaya Bello
EFCC ta ce ta kira Yahaya Bello a waya domin girmamawa. Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Shugaban ya yi bayani ne domin karin haske kan takaddamar da hukumar ke yi da tsohon gwamnan a kwanan nan.

A wani sako da EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, shugaban ya ce ya yi ƙoƙarin mutunta Yahaya Bello a matsayinsa na tsohon gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya faru tsakanin EFCC da Bello

A cewar shugaban, tun a karon farko ya kira Yahaya Bello ta wayar tarho saboda girmamawa amma hakan bai yi amfani ba.

A lokacin da aka kira shi ta waya domin ya kai kansa ofishin hukumar sai ya ce ba zai samu zuwa ba saboda 'yan adawa sun yi shirin ba shi kunya a bakin ofis din.

Duk da haka hukumar ta kara ba shi damar zuwa ofishin shugabanta a kebe domin tattaunawa, amma ya ki amsa gayyatar.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Shugaban EFCC na ƙasa ya sha alwashin yin murabus daga muƙaminsa

A karshe Yahaya Bello ya ce wa hukumar EFCC idan ta matsu sai dai ta zo har kauyensa ta same shi domin ya amsa tambayoyi.

Abin da ya faru a gidan Yahaya Bello

Har ila yau shugaban ya yi jawabi a kan yadda suka samu gidan Yahaya Bello a lokacin da suka yi yunkurin kama shi a bayan ya ki amsa gayyatar.

A cewarsa, dakarun EFCC sama da 50 sun isa gidan Yahaya Bello ne tun karfe 7.00 na safe a domin cafke shi.

Amma sai suka tarar da 'yan sanda sama da 30 suna dauke da makamai a kofar gidan. Dakarun na ƙoƙarin kutsawa gidan ne sai ga gwamnan Kogi ya iso ya cece shi.

Kotu ta ce a kama Yahaya Bello

A wani rahoton kuma, kun ji cewa, rahotanni sun yi nuni da cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta samu izinin kama Yahaya Bello.

Mai shari’a Emeka Nwite na babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ya ba EFCC takardar izinin kamun a yammacin Laraba, 17 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel