Tinubu Ya Ajiye Girma, Ya Roki 'Yan Najeriya game da Zaben 2027
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi al’ummar jihar Edo su sake zaɓensa a wa’adi na biyu domin ya kammala ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta fara
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, ya bayyana hakan a wajen gangamin kamfen ɗin jam’iyyar APC a birnin Benin
- Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka a fannonin tituna, wutar lantarki da kiwon lafiya a jihar, yana mai neman al’ummar Edo su ba shi damar kammala su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi al’ummar jihar Edo su sake zaɓensa a karo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairun 2027.
Tinubu, wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya yi wannan roƙo ne a ranar Alhamis yayin gangamin kamfen ɗin jam’iyyar APC a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa gangamin ya zo daidai da cikar gwamnatin Gwamna Monday Okpebholo shekara biyu a kan mulki, inda Shettima ya bayyana ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a jihar.
Tinubu ya lissafa ayyukansa a Edo
A jawabinsa, Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ta fara ayyukan raya ƙasa da dama a jihar, musamman a fannonin tituna, wutar lantarki da kiwon lafiya.
Ya lissafa aikin faɗaɗa titin Benin-Ekpoma, Benin-Auchi da Benin-Okene, da kuma gyaran gaggawa da ake yi a kan titin Benin-Asaba.
Punch ta wallafa cewa ya kuma bayyana cewa an kammala aikin bututun iskar gas na Obiafu-Obrikom-Oben, wanda zai taimaka wajen samar da wutar lantarki a ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce sabbin layukan wutar lantarki da ake ginawa za su iya ƙara megawatt 600 ga wutar lantarkin da ake samarwa a Najeriya.
Ya ce:
“Mun yi tafiya mai nisa tare da amincewarku, kuma muna neman damar ku don kammala aikin da muka fara.”
Magana kan kiwon lafiya a Edo
Shettima ya kuma ambaci cibiyar kula da masu cutar daji da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.
Ya ce gwamnati na tallafa wa cibiyoyin kula da lafiya na gwamnati 158 a faɗin Edo domin inganta harkokin kiwon lafiya.
A kan al’adun gargajiya, mataimakin shugaban ƙasar ya ce an samu ci gaba wajen dawo da kayan tarihi na masarautar Benin da aka kwashe zuwa ƙasashen waje.

Source: UGC
Ya bayyana cewa jami’o’in Cambridge da Sweden sun miƙa ikon mallakar wasu daga cikin kayan tarihin ga Najeriya.
Ya ce ya kamata a yi la’akari da tasirin ayyukan da gwamnati ta gudanar a rayuwar al’umma wajen tantance ayyukanta.
Tinubu ya godewa Jigawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Tinubu ya yi godiya ga al’ummar jihar Jigawa bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa.
Shugaban ƙasar ya kuma sha alwashin ƙarfafa rundunonin tsaron Najeriya ta hanyar inganta albashinsu da jin daɗinsu domin taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.
Tinubu ya kuma ƙaddamar da wasu kayayyakin noma a Jigawa, inda ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kawo nasarori har zuwa shekarar 2031.
Asali: Legit.ng

