Facebook zai fara tona asirin labaran karya

Facebook zai fara tona asirin labaran karya

Kamfanin sada zumunta na Facebook, ya sanar da aniyarsa ta shimfida sabbin matakai da za su agaza wajen yakar yaduwar zantuka na kazon kurege da shaci-fadi a shafukansa da dandalan sada zumunta.

A sabuwar sanarwar da kamfanin ya fitar, ya ce daga yanzu za'a rinka tantance labaran karya ta hanyar banbanta su da na gaskiya, wanda masu bin diddigin tushe da kuma gano asali suka tabbatar a shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram.

A baya-bayan nan ne kamfanin Facebook ya fadada shirinsa a kan bin diddigin labarai zuwa kasashe goma dake Kudu da hamadar Sahara a nahiyyar Afirka.

Kasashen goma sun hadar da Ghana, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Uganda, Burkina Faso, Somaliya, Zambiya, Habasha, Ivory Coast, Guinea da Tanzania.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, shugaban sashen manufofi a Afirka na kamfanin, Kojo Boake, ya ce a kokarin da aka ci gaba da yi na dakile duk wasu hanyoyon yaduwar labaran kanzon kurege, za a kaddamar da shirin ta hanyar cin moriyar juna da wasu abokanan hulda na kamfanin kamar su Africa Check, Pesa Check, Dubawa, France 24 da kuma AFP Fact Check.

KARANTA KUMA: Haramta Boko: 'Yan ta'adda sun kona makarantu a kasar Nijar

Ya ce "daukar matakai don hana labaran karya bazuwa a Facebook hakki ne da ya hau kanmu kuma dole mu dauke shi da muhimmanci, mun san cewa labaran karya sun zama matsala, kuma wadannan su ne matakai masu muhimmanci da muka dauka don shawo kan matsalar".

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel