El Rufai Ya Wanke Hadimansa, Ya Fadi Laifin da Ake Zarginsu da Aikatawa a Kaduna

El Rufai Ya Wanke Hadimansa, Ya Fadi Laifin da Ake Zarginsu da Aikatawa a Kaduna

  • Malam Nasir El-Rufai ya kare mukarrabansa, musamman Jimi Lawal, kan zargin badakala da ake yadawa a kansu yanzu
  • El-Rufai ya bayyana cewa zarge-zargen da ake yi ba su da tushe, kuma an shafe shekara ana bincike babu abin a zo a gani
  • Ya ce Jimi Lawal bai saci kudin Kaduna ba, domin kudinsa ma ya kashe kafin a biya shi, kuma akwai takardun hujjoji kan aikin
  • Tsohon gwamnan Kaduna ya caccaki hukumomi kan tsare mutum ba hujja, ya ce su jira Allah zai barsu su tsira kan haka ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya yi tone-tone kan zargin na kusa da shi da ake yi a halin yanzu.

Malam Nasir El-Rufai ya kare wasu daga cikin mukarrabansa ciki har da Jimi Lawal da ake tuhuma da badakala makudan kudi.

Kara karanta wannan

'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai

El-Rufai ya soki Uba Sani kan binciken gwamantinsa da ke yi
Nasir El-Rufai ya kare mukarrabansa kan zargin cin hanci da ake yi musu. Hoto: Nasir El-Rufai.
Asali: Facebook

El-Rufai ya wanke hadimansa daga zargin cin hanci

El-Rufai ya bayyana haka ne yayin hira da rediyon Freedom a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin YouTube.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, El-Rufai ya nuna damuwa kan yadda ake ta zarge-zarge da babu hujjoji inda ya ce duka kararrakin karya ne.

Tsohon gwamnan ya kare wasu daga cikin na kusa da shi musamman hadiminsa, Jimi Lawal kan tuhumarsa da ake yi.

El-Rufai ya ce a cikin faifan bidiyon:

"Duk karar da aka shigar kan Bashir Salisu da Jimi Lawal kwarya ce, Jimi kudinsa ya kashe amma ake cewa wai ya sace kudin Kaduna.
"Idan Jimi zai yi sata sai ya sace N64m don Allah, ko shugaban ƙaramar hukuma zai sace N64m?.
"Kuma a hakan akwai takardu da komai kafin fara aikin sannan akwai shaidar amincewa zai biyan kudinsa kafin aiki da aka biya shi.
El-Rufai ya kare wasu daga cikin mukarrabansa kan zargin cin hanci
Nasir El-Rufai ya nuna damuwa kan yadda ake kulle mutum a gidan yari babu hakkinsa. Hoto: Uba Sani, Nasir El-Rufai.
Asali: Twitter

El-Rufai ya kalubalanci hukumomi kan tsoron Allah

Kara karanta wannan

El Rufai ya tuno shekaru 8 na mulkinsa, ya fadi abubuwa 4 da ya fi jin dadinsu

El-Rufai ya koka kan yadda aka shafe shekara ana bincike amma ba a samu wani abin kirki ba saboda daman korafe-korafen karya ne.

Ya kara da cewa:

"Amma a ce an yi shekara ana bincike wai sai wannan abin ku ka iya ganowa wanda mun san asusun da kudin yake."
"Amma don iskanci da rashin tsoron Allah ku kama mutum ku kai shi gidan yari kwana 50 kun dauka Allah zai bar ku?

Tsohon gwamnan ya kuma tabo batun tuhumarsa da aka yi kan wasu zarge-zarge har na filaye a Abuja inda aka gaza samun nasara a kansa.

El-Rufai ya zargi Ribadu da yi masa makarkashiya

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi Nuhu Ribadu da shirya makarkashiyar tura shi gidan yari kafin zabe.

Nasir El-Rufai ya ce Ribadu na kokarin bata masa suna saboda tsoron ka da ya hana su cin nasara a zabukan da ke tafe musamman na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

"40% ake ba shi," El Rufai ya zargi Uba Sani da yin kashe mu raba da ƴan kwangila

Tsohon gwamnan ya zargi cewa an ba Gwamna Uba Sani kwangilar rubuta rahoto na bogi don kai shi kasa, bisa umarnin Ribadu da ke takun-saka da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel