Kano: 'Yan Siyasa 5 da Za Su Iya Zama Barazana ga Abba Gida Gida a Zaben 2027

Kano: 'Yan Siyasa 5 da Za Su Iya Zama Barazana ga Abba Gida Gida a Zaben 2027

  • An fara daura damarar fafatawa a zaben 2027 a Kano, inda jam’iyyun NNPP da APC ke karbar masu sauya sheka don karfafa kansu
  • Ana hasashen Abba Kabir Yusuf zai nemi tazarce da goyon bayan Rabiu Kwankwaso, yayin da APC za ta dogara da gwamnatin tarayya
  • Sanata Barau Jibrin, Nasiru Gawuna, na cikin 'yan siyasa biyar da ake ganin za su iya ba Abba matsala a neman tazarcensa a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Duk da cewa sai nan da kusan shekaru biyu za a gudanar da zaben 2027, amma tun yanzu, manyan ‘yan siyasar Kano sun fara shirin fafatawa.

Jam’iyyar NNPP mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta APC suna ta karbar ‘yan siyasa da suka sauya sheka daga sauran jam’iyyu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, an yi hasashen shirin tumbuke Tinubu

Rahoto ya yi bayanin 'yan siyasa 5 da za su iya neman kujerar Abba Yusuf a zaben 2027
Rahoto: Ana hasashen wasu 'yan siyasar Kano 5 za su neman kujerar Abba a zaben 2027. Hoto: @barauijibrin, @DGawuna_, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Yadda APC da NNPP ke shiryawa zaben 2027

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Gwamna Abba Yusuf zai iya yin amfani da karfin mulki domin neman wa’adi na biyu, yayin da APC za ta dogara da goyon bayan gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kyautata zaton NNPP za ta tsayar da Gwamna Abba don neman tazarce, yayin da APC ke iya tsayar da sabon dan takara ko kuma Nasiru Yusuf Gawuna.

Alamu sun nuna wasu ‘yan siyasa a Kano sun fara neman matsayi mai kyau domin samun nasara a 2027.

A jam’iyyar APC, manyan masu neman takara sun hada da Sanata Barau Jibrin, Nasiru Yusuf Gawuna, Abba Bichi, Murtala Sule Garo da Inuwa Waya.

Siyasar Gwamna Abba da neman tazarce

Gwamna Abba Yusuf yana da karfin mulki tare da cikakken goyon bayan tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

An san Gwamna Yusuf da lakabin "Abba Gida Gida," kuma sunansa ya na da matukar farin jini a jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

Bayan darewarsa kan mulki, ya fara aiwatar da alkawuran yakin neman zabensa domin inganta rayuwar Kanawa.

Yana da ikon gudanar da jam’iyyar NNPP a matakin jiha tare da shugabanci a kananan hukumomi 44 na jihar.

Abin da zai iya zama kalubale a gare shi shi ne batun rusau da gwamnatinsa ta fara yi a farkon hawansa mulki a 2023.

Wani kalubalen shi ne kiraye-kirayen wasu da ke neman ya zamo mai cikakken ikon mulki ba tare da jingina da Kwankwaso ba, watau 'tsaya da kafarka Abba.'

Wannan kiraye-kiraye ya ya haifar da baraka, wanda har ake zargin shi ne silar tsige Abdullahi Baffa Bichi daga mukamin sakataren gwamnatin jihar.

A lokacin da gwamnati ta sallami Bichi, an ce zai tafi ne saboda dalilan lafiya, yayin da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol, ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi jihar da suka shirya kwatowa, ya lissafa nasarorin Tinubu

Wasu mambobin NNPP sun fice daga Kwankwasiyya ko kuma suka janye daga harkokin gwamnati gaba daya, wanda ka iya zama kalubale ga Abba.

'Yan siyasar da za su iya yakar Abba

Legit Hausa ta yi nazarin wasu 'yan siyasa da za su iya ba Abba Gida-Gida ciwon kai a yayin neman tazarce a 2027:

1. Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, na daga cikin manyan masu neman takarar gwamna karkashin APC.

Yana wakiltar mazabar Kano ta Arewa a majalisar dattawa kuma a halin yanzu, yana daga cikin masu tsonewa NNPP ido a Kano.

Sanata Barau ya yi ayyuka da dama da suka inganta rayuwar al’umma a fadin Kano. Wadannan ayyuka sun ba shi karbuwa da gagarumar dama a APC.

Har zuwa yanzu, yana ci gaba da karbar ‘yan siyasa daga NNPP da sauran jam’iyyu zuwa APC, kuma ana hasashen jam'iyyar na iya ba shi tikitin takara.

Kara karanta wannan

"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura

2. Nasiru Yusuf Gawuna

Nasiru Yusuf Gawuna ya taba zama mataimakin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma ya samu karbuwa ga magoya bayan tsohon gwamnan.

A zaben shekarar 2023, Ganduje ya zabe shi a matsayin dan takarar gwamna na APC duk da adawar wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Yana da damar sake samun wannan goyon bayan na Ganduje a 2027, kasancewarsa shugaban jam’iyyar APC na kasa a yanzu.

Amma rashin bayyana kansa, ko gudanar da wasu harkokin siyasa tun bayan zaben 2023 na iya zama matsala ga Nasiru Gawuna.

3. Abubakar Bichi

Abubakar Bichi shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi a majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin kasafin kudi.

Ya samu karbuwa saboda kyautarsa ga al’umma, wanda ya sa ya zama daya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan Kano a APC.

Ana ganin cewar kwarewar Abubakar Bichi da yadda yake son kyautatawa Kanawa na iya sa ya samu tikiti, wanda zai zama kalubale ga Abba.

Kara karanta wannan

Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano sun shafe shekara 1 babu 'dan majalisar dokokin jiha

4. Murtala Sule Garo

Murtala Sule Garo ya kasance mataimakin Gawuna a zaben 2023, kuma na hannun damar tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje.

Duk wata gwagwarmaya da Ganduje da Gawuna suka yi, to Murtala na tare da su, kuma an ce yana da matsayi babba a wajen uwar gidan Ganduje.

Ana ganin cewa yana da niyyar neman kujerar gwamna a 2027 bayan hakura da tikitin 2023, wanda idan hakan ta tabbata, zai kara zama matsala ga Abba.

5. Inuwa Waya

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa Alhaji Inuwa Waya ya yi ritaya daga NNPC domin neman tikitin gwamna a 2023 karkashin APC.

Ya fadi takarar ne saboda Ganduje ya zabi Gawuna a matsayin dan takara, tun daga nan kuma ba a sake jin duriyarsa a harkokin siyasar jihar ba.

Sai dai ana ganin kamar Alhaji Inuwa ya yi irin abin nan da ake cewa: 'Ja da baya ba tsoro ba, gyaran taku ne,' kuma ana tunanin zai sake neman takara a 2027.

Kara karanta wannan

An kama 'yan bindigar da suka ba basarake kudi domin kafa sansanin ta'addanci

Kalubalen da APC za ta fuskanta

Babban kalubalen da ake ganin APC za ta fuskanta shi ne rikicin cikin gida tsakanin Abdullahi Ganduje da Barau Jibrin kan ikon jam’iyya a Kano.

Haka kuma, wasu manufofin gwamnatin APC a matakin tarayya da ake ganin suna cutar da talakawa na iya shafar jam’iyyar.

A zaben 2023, APC ta sha kaye a hannun NNPP saboda rikicin cikin gida da kuma guguwar 'Abba Gida-Gida' da tasirin Kwankwaso.

Nasarar APC a 2027 za ta dogara ne da yadda ta shawo kan matsalolin cikin gida da kuma yadda za ta kyautatawa talakawa kafin lokacin zaben.

Barazana daga cikin gidan NNPP

Itama jam'iyyar NNPP mai mulki, na da nata matsalolin, ciki har da rashin jituwar kusoshin jam'iyyar da shugabansu, Dakta Hashimu Dungurawa.

Baya ga bangaren Hashimu Dungurawa na Kwankwasiyya, akwai tsagin Barista Dalhatu Shehu da ke da'awar su ne asalin yan NNPP.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

Sannan, a baya bayan nan, wasu 'yan NNPP sun yi korafin ba a yi musu adalci ba wajen raba mukamai da damar shugabanci, lamarin da ya jawo ficewar wasu daga jam’iyyar.

Ana ganin ficewar wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar saboda rashin gamsuwa da tsarin shugabanci na iya rage karfin NNPP a jihar.

"NNPP za ta rage tasirin APC a Kano" - Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce NNPP za ta rage karfin jam'iyyar APC kafin zaben 2027.

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na NNPP a Kano, Sanata Kwankwaso ya ce APC ba za ta samu fiye da kuri’u 15,000 a zaben 2027 a jihar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.