Muhimman Ayyuka 15 da Gwamnatin Abba Tayi Cikin Shekara 1 a Jihar Kano

Muhimman Ayyuka 15 da Gwamnatin Abba Tayi Cikin Shekara 1 a Jihar Kano

  • Abba Kabir Yusuf yana cikin gwamnonin da suka cika shekara da hawa mulki, ya shafe watanni 12 a madafun iko
  • Ayyukan gwamnatin Abba sun ratsa bangaren ilmi, taimakon al’umma, kula da ma’aikata da ayyukan more rayuwa
  • Gwamnan Kano kadai yake rike da tutar jam’iyyar NNPP, ya yi nasarar raba APC da mulkin Jihar Kano a zaben 2023

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A karshen watan da ya gabata, sababbin gwamnonin jihohin da aka zaba a farkon 2023 suka cika shekara guda a ofis.

Daga zamansa gwamna bayan ya gaji Abdullahi Umar Ganduje, Abba Yusuf ya kawo wasu ayyukan cigaba da-dama a jihar Kano.

Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shekara 1 a Kano yana mulki Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin Abba Kabir ta shekara a mulki

Duk da nasarorin gwamnatin NNPP, ana fama da wasu kalubale kamar matsalar ruwa wanda ake sa ran a magance matsalar.

Kara karanta wannan

Matakai 10 da Gwamna Abba ya dauka wajen ayyana dokar ta baci a kan ilmi a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin ayyukan da za su a yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf sun hada da biyan fansho da giratuti bayan shekaru.

Bayan tsofaffin ma’aikata, gwamnatin Abba ta taba zaurawa da ‘yan matan da aka aurar da su a karkashin tsarin auren gata.

Ayyukan gwamnatin Abba a Kano

1. Tura dalibai zuwa makarantun kasashen waje

2. Biyan giratuti da fanshon tsofaffin ma’aikata

3. Aurar da zaurawa da ‘yan mata

4. Biyan kudin makarantar wasu daliban Kano da ke jami’o’in gida

5. Rage kudin karatu a manyan makarantun gwamnatin jiha

6. Biyan kudin jarrabawar kammala shiga sakandare

7. Bude makarantun koyon sana’o’in da aka yi watsi da su

8. Karbo da gyaran manyan asibitocin gwamnatin Kano

9. Fara aikin gadojin sama a Dan Aguni da Tal’udu

10. Kwangilolin tituna a cikin unguwanni

11. Farfado da tsarin gina titunan kilomita 5 a kananan hukumomi

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya fadi abin da ya dauke hankalin Abba a shekara 1 na mulki

12. Tallafawa mata da masu kananan kasuwanci

13. Haskaka titunan garin Kano

14. Yunkurin daina zaftare albashi da sauran hakkokin ma’aikata

15. Taimakawa marasa lafiya da maganguna da kula kyauta

Abin da Abba Kabir ya sa a gaba

Da Legit Hausa ta zanta da Hassani Sani Tukur, ya shaida mata cewa a tsarin gwamnatin Kwankwasiyya, ilmi ne a kan gaba.

Hassan Tukur yana cikin masu taimakwa gwamnan jihar Kano a shafin sadarwa ya ce inganta ilmi shi ne burin Abba Kabir Yusuf.

A cewarsa, ilmi yana da muhimmanci kuma sun fahimci da haka ne za a yi maganin mafi yawan matsalolin da suka addabi kasar nan.

Abba zai bunkasa ilmi a Kano

A yammacin jiya ne aka ji labari Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa dokar ta-baci, zai gyara makarantu kuma zai gina aji 10, 000 a Kano.

An fara da kara kason ilmi a kasafin kudin 2024, za a bude makarantun da aka rufe kuma gwamnatin Kano ta dauki malaman BESDA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel