Babban Jami’in NNPC zai ajiye aikinsa mai tsoka, yana harin kujerar Ganduje a zaben 2023

Babban Jami’in NNPC zai ajiye aikinsa mai tsoka, yana harin kujerar Ganduje a zaben 2023

  • Inuwa Waya ya rubuta takarda, ya ajiye aikinsa a kamfanin mai na NNPC
  • Duk da yana da sauran shekaru biyu, Waya yace lokacin hutawar sa ya yi
  • Masu hasashen suna ganin Waya zai shiga siyasa, ya yi takara a jihar Kano

Abuja - Babban manajan NNPC da ke kula da harkar jigila da dakon kaya ta ruwa, Inuwa Waya ya bada sanarwa zai ajiye aikinsa a kamfanin mai na kasa.

A ranar Lahadi, jaridar Premium Times ta samu labarin murabus din da Inuwa Waya yayi, duk da cewa kamfanin bai bayyana wannan cigaba da aka samu ba.

Inuwa Waya ya rubuta takardar murabus, yace zai ajiye aiki a karshen watan Disamban shekarar nan.

Inuwa Waya ya fara hutun barin aiki

Kara karanta wannan

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

Majiyoyi da dama sun sanar da jaridar cewa Waya ya rubuta takardar ajiye aiki a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, 2021, duk da bai cika shekaru yin ritaya ba.

Wani babban jami’in NNPC da ya samu labarin abin da ya faru, ya shaida cewa tuni har Waya ya fara hutun watanni uku da ake yi kafin ma’aikaci ya yi ritaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban Jami’in NNPC
Alhaji Inuwa Waya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahoton yace Alhaji Waya ya sanar da abokan aikinsa cewa ba zai cigaba da aiki a NNPC ba. Waya ya bayyana haka ne a bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

A ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba, 2021, Waya ya yi bikin cika shekara 58 da haihuwa a Duniya.

Ya kamata a bar wa yara aiki a NNPC

“Tsawon shekaru 30 ina aiki a NNPC a wurare dabam-dabam. A wannan lokaci da nayi, na yi imani nayi bakin kokari wajen bada gudumuwa ta a hukumar.”

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

“Komai yana da lokacinsa; akwai lokacin wasa, akwai lokacin daina aiki domin mutum ya huta saboda ya samu ya cin ma sauran burace-buracen rayuwa.”

An fara shirya wa siyasar 2023

Ana zargin cewa Waya wanda ya zo NNPC a 1989 ya ajiye aiki ne da nufin ya shiga siyasa. Bisa dukkan alamu yana da niyyar ya yi takarar gwamna a jihar Kano.

Kwanakin baya an ji cewa har an fara hasashe kan wadanda ake ganin za su tsaya takarar gwamna a jam’iyyar APC bayan wa’adin Abdullahi Ganduje a zaben 2023.

Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya da takwaransa mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin su na cikin wadanda ake ganin suna da sha’awar neman Gwamnan Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel