Ganduje ya raba gardamar APC a Kano, ya tsaida wanda zai gaje kujerarsa a zaben 2023

Ganduje ya raba gardamar APC a Kano, ya tsaida wanda zai gaje kujerarsa a zaben 2023

  • Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana wanda yake so ya zama magajinsa a zabe mai zuwa
  • Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Gawuna shi ne wanda Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake so
  • An cin ma wannan matsaya ne a wajen wani taron jagororin jam'iyyar APC mai mulki na jihar Kano

Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Gawuna shi ne wanda ake tunanin zai rike tutar APC a zaben gwamnan Kano da za ayi a 2023.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu 2022 da ya bayyana cewa Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tsaida zabinsa.

Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana Nasir Gawuna ne a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Masu ruwa da tsakin na APC mai mulki sun kuma yarda Alhaji Murtala Sule Garo ya yi takarar kujerar mataimakin gwamna a karkashin jam’iyyar.

Murtala Sule Garo shi ne ya rike kujerar kwamishinan kananan hukumomi a gwamnatin Ganduje. Jaridar Gandujiyya Online ta kawo rahoton.

Murtala Sule Garo yana cikin wadanda suke da karfi a jam’iyyar APC mai mulki a halin yanzu. Garo ya kafa mabiya a duka kananan hukumomi 44.

Dr. Nasir Gawuna da Murtala Sule Garo
Dr. Nasir Gawuna da Murtala Sule Garo Hoto: @gandujiyyaonline
Asali: Facebook

Gwamna zai fito daga Kano ta tsakiya?

Yayin da Gawuna ya fito daga karamar hukumar Nasarawa a yankin Kano ta tsakiya, Garo ya fito ne daga karamar hukumar Kabo a kudancin Kano.

Kafin zamansa mataimakin Gwamna bayan Farfesa Hafizu Abubakar ya yi murabus a 2018, Gawuna ya taba rike mukamin Kwamishina a baya.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Jaridar ta ce idan Dr. Gawuna ya yi nasarar zama gwamna a zaben 2023, za a maimaita abin da ya faru ne a 2015, inda mataimaki ya gaji mai gidansa.

Ganduje shi ne mataimakin gwamna a lokacin da Rabiu Kwankwaso yake mulki a Kano. Bayan kai ruwa rana aka yarda a ba shi tutan APC a lokacin.

"Allah ya sa zabin Allah ne"

Jagoran APC a Kano, Ismail Ahmed ya tabbatar da wannan batun, ya ce ya ji dadin zabin da aka yi.

"Nayi farin cikin samun labarin zabin gwamnan jihar Kano na ayyana magajinsa. Dr. Nasiru Yusuf Gawuna."
"Ina matukar farin ciki.Allah ya sa zabin Allah ne." - Ismail Ahmed.

Zabin Murtala Sule Garo

Tun ba yau ba aka taba jin labarin Mai dakin gwamnan Kano, Hafsat Ganduje ta na nuna cewa tana goyon bayan irinsu Murtala Garo su karbi mulki a 2023.

Da ta ke magana a wajen wani taro a karamar hukumar Ungogo, Hafsat Ganduje ta ce Murtala Sule Garo ya fi dacewa da mulki saboda kokarin da ya ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel