Akwai aiki: Mai harin Gwamna a APC bai yarda da zabin da Ganduje ya yi na dauko Gawuna ba

Akwai aiki: Mai harin Gwamna a APC bai yarda da zabin da Ganduje ya yi na dauko Gawuna ba

  • Inuwa Waya ya ce zai gwabza da Nasiru Yusuf Gawuna a takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar APC
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zabi a ba Nasiru Gawuna tikitin jam’iyyar APC a zaben 2023
  • Waya mai neman zama Gwamnan jihar Kano ya nuna babu ruwan shi da matakin da aka dauka

Kano - Inuwa Waya wanda yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen neman gwamna a jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC ba zai fasa yin takara a 2023 ba.

Daily Nigerian ta rahoto Inuwa Waya yana nuna zai kalubalanci matsayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dauka na fito da wanda yake so ya gaje shi.

Waya ya shaidawa jaridar zai saye fam din neman shiga takarar gwamna a jam’iyyar APC mai mulki, duk da gwamna yana tare da Nasiru Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

“A ayyana mutum a matsayin ‘dan takara dabam, sannan kuma ya zama wanda zai rikewa jam’iyya tuta a zabe dabam.”
“Ina nan a takara, matakin da aka dauka ba zai kawo mana cikas wajen kawowa Kano shugabanci mai nagarta ba.”
“Mu na sa ran cewa jam’iyyar APC za ta bada dama ga dukkan wani mai neman takara ya wanke allonsa, ya nemi kujera.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Inuwa Waya
Jigon APC, Inuwa Waya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Mun yi imani mu na da abin da ake bukata wajen samun tikitin tsayawa takara, sannan kuma mu lashe babban zabe.”
“Mun yi imani mu na da abin da ake bukata wajen samun tikitin tsayawa takara, sannan mu lashe babban zabe.” - Inuwa Waya.

A yau ake sa rai Waya zai saye fam a sakatariyar APC, ya kuma yi kira ga magoya bayansa su jajirce domin ganin ya samu nasara a zaben tsaida ‘dan takara.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Alakar Waya da Ganduje

Har ila yau, kwararren Lauyan ya shaidawa Daily Nigerian cewa Mai girma Abdullahi Ganduje uba yake gare su a siyasa, don haka zai bada dama ayi adalci.

Burin mai neman takarar shi ne Gwamna Ganduje ya nuna dattaku a zaben fitar da gwanin na APC.

Tsohon ma’aikacin na NNPC ya karyata rade-radin cewa gwamna ya tunkare shi a dalilin makudan kudin da yake kashewa domin ya samu tikiti a APC.

Gawuna: APC ta nemi sauki ne

Legit.ng Hausa ta yi magana da Adnan Mukhtar Tudun Wada, ‘dan siyasa mai neman kujerar ‘dan majalisar dokokin Kano a jam’iyyar PDP a kan batun 2023.

Tudun Wada ya ce a tunaninsa Nasiru Gawuna shine wanda yafi zama masalaha cikin duk masu son zama Gwamna a APC domin shi ba ya rikici da kowa.

Matashin yana sa ran jam’iyyarsu ta PDP ta doke Gawuna, wanda a na sa hange, ba wanda ya saba cin zabe bane, sannan bai da abin kirkin da zai nuna.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Asali: Legit.ng

Online view pixel