Tsohon Gwamnan PDP Ya Fadi Umarnin Mahaliccinsa kan Takara a Zaben 2027

Tsohon Gwamnan PDP Ya Fadi Umarnin Mahaliccinsa kan Takara a Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan Binuwai, Samuel Ortom ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara a zaben 2027 ba
  • Ya ce ko a baya, rashin tuntubar Ubangijinsa ne ya hana shi cin nasara a zaben da ya gabata watau na 2023
  • Ortom ya jaddada cewa PDP na kulla kyakkyawan shiri kan kujerar gwamnan Binuwai a zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Binuwai, Cif Samuel Ortom ya bayyana cewa Mahaliccinsa ya ba shi sako kan takara a babban zaben kasar nan na shekarar 2027.

Tsohon gwamnan, wanda ya fadi neman zaben Sanata a jiharsa a 2023 ya bayyana haka ne lokacin da wasu kusoshin PDP na G-14 su ka ziyarce shi a Makurdi.

Kara karanta wannan

Zargin N27bn: Bayanai sun fito da hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamna

Ortom
Tsohon gwamna Samuel Ortom ya ce ba zai tsaya takara ba Hoto: Sagacious Bello Lukman
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa yan G-14 na PDP a Binuwai na wakiltar dattijan kananan hukumomi 14 da ke yaren Tiv a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ortom: Tsohon gwamna ba zai yi takara a 2027 ba

Tsohon gwamnan Binuwai, Samuel Ortom ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a shekarar 2027 ba saboda bin umarnin mahaliccinsa.

Daily Post ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya fadi zaben 2023 ne saboda mai nemi taimakon Ubangijinsa a lamarin ba.

"Za mu kwato kujerar gwamnati:" Tsohon gwamnan Binuwai

Tsohon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya ce su na cikin shirin kwace kujerar gwamnan jiharsa a zaben 2027 mai zuwa.

Ya kara da cewa Ubangijinsa ya fada masa komai, kuma ya umarce shi da ya jira umarni na gaba kan batun takara a zaben kasar nan.

Kara karanta wannan

Mutuwar matar gwamna: An shiga jimami, PDP ta dakatar da yakin neman zabe

Sakon Ortom ga tsohon gwamna Yahaya Bello

A baya kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya shawarci takwaransa na Kogi, Yahaya Bello da ya mika kansa ga hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC).

Hukumar EFCC na zargin Yahaya Bello da kassara baitul malin jiharsa a lokacin ya na gwamna, inda ake zargin ya wawashe wasu makudan kudin da sun kai N80.2bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.