Akwai Kitimutmura a 2027: Tawagar G5 Ta PDP a Ta Marawa Shugaba Tinubu Baya a Zaben 2027, Inji Ortom

Akwai Kitimutmura a 2027: Tawagar G5 Ta PDP a Ta Marawa Shugaba Tinubu Baya a Zaben 2027, Inji Ortom

  • Gwamnonin G5 sun bayyana goyon bayansu da mubaya'a ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na Najeriya
  • Gwamnonin na PDP sun bayyana cewa, a shirye suke su ba da duk mai yiwuwa wajen tabbatar da Tinubu ya yi tazarce
  • An sha kitimurmura tsakanin 'yan G5 da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 da ya gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa kungiyarsu ta G5 mai adawa da tafarkin uwa jam’iyyar PDP za ta marawa shugaban kasa Bola Tinubu baya a zaben 2027.

Kungiyar G5 dai gungun wasu gwamnoni ne da suka hada da Ortom, Wike, Ugwuanyi, Okezie Ikpeazu (Abia) da Seyi Makinde (Oyo).

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

Dukkan ‘ya’yan tawagar sun kammala wa’adin mulkinsu na biyu na shekaru takwas a watan Mayun da ya gabata idan aka cire Makinde da ke kan wa’adinsa na biyu a yanzu.

Gwamnonin G5 sun ce za su goyi bayan Tinubu a 2027
Zaben 2027: 'Yan G5 na bayan Tinubu | Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ortom yayi magana ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu, a wajen wani taron liyafar cin abincin rana da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya shirya a Rivers, rahoton The Nation.

Ya tabbatar da cewa ‘yan G5 ba su da nadamar bayyana goyon bayan nasarar Tinubu a zaben da ya gabata, inda ya bayyana cewa tawagar za ta sake marawa tsohon gwamnan na Legas baya a karo na biyu a matsayin shugaban Najeriya a 2027.

Ortom ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Tinubu zai gyara harkokin tsaro, tattalin arziki da sauran muhimman abubuwan da ke fuskantar kalubale ga ‘yan kasar a wa’adin mulkinsa, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Muhimman abubuwa 10 da suka faru a Majalisar Tarayya a shekarar da ta wuce

Bayanai daga bakin tsohon gwamna Ortom

A cewar Ortom:

“Tuni shugabanmu, Nyesom Wike, ya bayyana cewa a 2027, za mu goyi bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
“Ba mu da inda za mu je domin abin da ‘yan Najeriya suka yi imani dashi kenan. Hatta gwamnatin da ta shude da ta durkusar da Najeriya daga sama har kasa, mun ba su damar yin mulki na tsawon shekaru takwas.
"Don haka, me zai hana gogaggen shugaba kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mulke mu tsawon shekaru takwas."

A dunkule G5 take

A wani labarin, Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom, sun ce babu wata rabuwar kai a tawagar gaskiya watau G5 da ta balle daga PDP, har yau kansu a haɗe yake.

Gwamnonin biyu sun bayyana cewa nan ba da jimawa ba G5 zata sanar da dan takarar shugaban kasan da zasu marawa baya a zabe mai zuwa a watan Fabrairu, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel