Wani Jigon NNPP Ya Kare Kansa, Ya Jero Dalilansa na Caccakar Shugaba Tinubu

Wani Jigon NNPP Ya Kare Kansa, Ya Jero Dalilansa na Caccakar Shugaba Tinubu

  • Ambasada Olufemi Ajadi ya musanta jita-jitar da ke cewa ya tsani shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu saboda yawan sukar da yake masa
  • Jigon na NNPP ya ce mutane sun masa gurguwar fahimta amma kaunar Tinubu ya sa yake yawan faɗa masa gaskiya komai ɗacinta
  • Ya ce burinsa shugaban kasar ya bar ayyukan alherin da za a rika yabonsa bayan ya sauka daga mulkin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Wani jigon NNPP, Ambasada Olufemi Ajadi ya kare kansa kan yawan sukar da yake yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ajadi ya bayyana cewa yana yawan caccakar Shugaba Tinubu ne domin ya taimaka masa ya sauke nauyin da Allah ya ɗora masa, ba wai don ya tsane shi ba.

Kara karanta wannan

"Ba Allah ya kawo mana talauci ba," Tsohon shugaban ƙasa ya ja kunnen shugabanni

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Wani jigon NNPP ya bayyana dalilin da yasa yake yawan caccakar gwamnatin Bola Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Ambasada Ajadi ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajadi ya musanta tsanar Bola Tinubu

'Dan siyasar ya kuma yi watsi da rade-radin cewa yana yawan sukar gwamnatin APC ne saboda ƙiyayyar da yake yi wa shugaban ƙasa Tinubu.

Olufemi Ajadi ya jaddda cewa haramun ne a kasar Yarbawa mutum ya tsani dattijo, ya kara da cewa abin da ya ke yi suka ce mai ma'ana don taimakawa Tinubu ya yi nasara.

Jigon NNPP ya jero dalilan sukar Tinubu

"Ni ban tsani shugaban ƙasa ba, asali ma ina ƙaunarsa a matsayinsa na shugabanmu, na damu ina so ya bar wani abin kirki da za a tuna da shi bayan ya bar mulki.
"Kowa ya sani watarana (Tinubu) zai sauka daga mulki kuma duk abin da ya yi zai shiga kundin tarihin ƙasa. Ba zan tsani shugaba na wanda yake ɗan ƙabilata ba.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

"Shugaba Tinubu na daya daga cikin jagororin Yarbawa, idan ya yi nasara, mu ne muka yi nasara, Hanyar da zan ba da gudummawata ita ce a koyaushe na gaya masa gaskiyar da yake buƙatar sani don samun nasara."

- Ambasada Ajadi.

Jigon NNPP ya ƙara da cewa galibin muƙarraban da ke kewaye da shugaban ƙasa ba za su faɗa masa gaskiya ba, shiyasa ya zaɓi ya riƙa gaya masa gaskiya komai ɗacinta, rahoton Tribune.

Matsalar tsaro: Bwala ya zargi ƴan siyasa

A wani rahoton kuma Daniel Bwala ya yi ikirarin cewa manyan ƴan siyasar da suka sha kashi a zaɓen 2023 suna da hannu a taɓarɓarewar tsaron Najeriya

Tsohon kakamin kamfen Atiku/Okowa 2023 ya nuna goyo baya ga kalaman tsohuwar mi kuɗi da ta ce rashin tsaro ya zama makamin ƴan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262