Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan PDP Ya Yi Nisa Bayan Majalisa Ta Dauki Sabon Mataki

Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan PDP Ya Yi Nisa Bayan Majalisa Ta Dauki Sabon Mataki

  • Kwamitin mutum bakwai da alƙalin alƙalan jihar Edo zai kafa, zai duba jerin zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu
  • Sakamakon binciken da kwamitin ya samu zai tabbatar da makomar Shaibu, inda ko dai majalisar ta tsige shi ko ya tsira da kujerarsa
  • Majalisar ta zargi mataimakin gwamnan na Edo da rashin ɗa’a da kuma bayyana bayanan gwamnati ba tare da izini ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Benin, jihar Edo - Majalisar dokokin jihar Edo a ranar Talata, ta umurci alƙalin alƙalan jihar, mai shari’a Daniel Okungbowa, da ya kafa kwamitin mutum bakwai da zai binciki zargin da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

Majalisar dokokin jihar na zargin mataimakin gwamnan da rashin ɗa’a da kuma bayyana bayanan gwamnati ga jama'a.

Za a kafa kwamitin binciken Philip Shaibu
Majalisar dokokin jihar Edo na da zarge-zarge a kan Philip Shaibu Hoto: Rt. Hon. Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Shaibu: Wane aiki kwamitin zai yi?

Ana sa ran kwamitin zai gudanar da cikakken bincike kan zargin tare da bayar da shawarwarin da suka dace, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar, RT Hon Blessing Agbebaku ne ya jagoranci zaman majalisar na ranar Talata, 19 ga watan Maris, 2024.

Ƴan majalisa 19 daga cikin 24 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙudurin kafa kwamitin binciken mataimakin gwamnan, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

Wani zargi ake yi wa Philip Shaibu?

Idan ba ku manta ba dai, majalisar dokokin jihar Edo, a farkon wannan watan, ta fara yunƙurin tsige Shaibu, inda ta zarge shi da saɓa kundin tsarin mulki.

Sai dai Shaibu ya musanta cewa an ba shi sanarwar tsige shi daga majalisar dokokin jihar kamar yadda kakakin majalisar, Hon. Agbebaku ya yi iƙirari lokacin zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Majalisar dattawa ta yi martani kan harin, ta fadi matakin dauka

A cewar shugaban majalisar, rashin karɓar sanarwar da Shaibu ya yi, ya sanya ta sauya salo wajen bada sanarwar tsige shi a manyan jaridun ƙasar nan.

Laifuffukan Philip Shaibu a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Edo ta jero tarin laifuffukan da ake zargin mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya aikata.

Majalisar ta zayyano laifukan Shaibu ne bayan ta fara shirin tsige shi daga muƙaminsa na mataimakin gwamna.

Daga cikin laifuffukan nasa akwai bayar da shaidar ƙarya da kuma cin amana ta hanyar sakin bayanan gwamnayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel