Hukumar Zabe INEC Ta Sanya Ranakun Zaben Gwamna a Jihohin Edo da Ondo

Hukumar Zabe INEC Ta Sanya Ranakun Zaben Gwamna a Jihohin Edo da Ondo

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanya ranakun zaben gwamnonin jihohin Edo da kuma Ondo a shekara mai zuwa 2024
  • Wa'adin gwamnan Edo zai ƙare ne ranar 11 ga watan Nuwamba, 2024 yayin da gwamnan Ondo zai sauka 23 ga watan Fabrairu, 2025
  • INEC ta fitar da cikakken jadawalin yadda za a gudanar da harkokin zaɓen jihohin tun daga zaben fidda gwani, kamfe da ranar fafata zaɓe

FCT Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta zaɓi ranakun da zata gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Edo da kuma Ondo a shekara mai zuwa 2024.

A sanarwan da ta wallafa a shafinta na manhajar X, INEC ta sanya ranar 21 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar da zata gudanar da zaben gwamna a jihar Edo da ke Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Jerin Fastocin Da Suka Yi Hasashen Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

Hukumar zabe INEC ta sa ranakun zaben gwamna a Edo da Ondo.
Hukumar Zabe INEC Ta Sanya Ranakun Zaben Gwamna a Jihohin Edo da Ondo Hoto: INECNigeria
Asali: UGC

Haka zalika hukumar ta zaɓi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024 a matsayin ranar zaɓen gwamma a jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar zaɓe INEC na ƙasa, Sam Olumekun, shi ne ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata, 26 ga watan Satumba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe wa'adin gwamnonin Edo da Ondo zai ƙare?

Ya ƙara da cewa wa’adin gwamnonin jihohin Edo da Ondo zai kare ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2024 da 23 ga Fabrairu, 2025, bi da bi.

Olumekun ya ce kamar yadda sashe na 178 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, za a gudanar da zaben gwamnonin ƙasa da kwanaki 150 kafin cikar wa’adin kuma kada ya gaza 30 gabanin saukar me riƙe da ofishin.

A cewarsa, mafi ƙarancin ranar da za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Edo ita ce 12 ga watan Oktoba, yayin jihar Ondo kuma ya kasance 23 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

APC Ta Samu Nasara, Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna a Zaben 2023

Bugu da ƙari, sashe na 28(1) na dokar zabe, 2022 ya bukaci hukumar INEC ta fitar da sanarwar ranar zaben kasa da kwanaki 360 kafin ranar zaben, inji shi.

Bayan haka INEC ta bayyana lokutan da jam'iyyu zasu gudanar da zaɓen fidda gwani, lokutan kamfe da sauran abubuwan da suka shafi zaɓen.

"An wallafa cikakken jadawalin yadda zabukan biyu zasu gudana a shafin yanar gizo na INEC da shafukan sada zumunta."
"Bisa wannan sanarwa kamar yadda kundin tsarin mulki da kuma dokar zabe suka tanada, hukumar na kira ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara da su lura da abubuwan cikin jadawalin kana su yi biyayya," in ji shi.

Kotu Ta Kori Karar PDP da Sandy Onor Kan Zaben Gwamnan Jihar Cross River

A wani rahoton na daban Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu.

Kotun zabe ta ƙara tabbatar da nasarar Gwamna Otu bayan ta kori ƙarar PDP da ɗan takararta saboda rashin cancanta.

Kara karanta wannan

Shugabar Karamar Hukumar da Ya Zargi Gwamnan APC da Wawure Kuɗi Ya Shiga Sabuwar Matsala

Asali: Legit.ng

Online view pixel