Dakatar da Ganduje Karo Na Biyu: APC Ta Mayar da Martani Mai Zafi Ga ’Yan Tawaren Jam’iyyar

Dakatar da Ganduje Karo Na Biyu: APC Ta Mayar da Martani Mai Zafi Ga ’Yan Tawaren Jam’iyyar

  • Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta sake yin martani kan dakatar da Abdullahi Ganduje daga jam'iyyar da aka yi a karo na biyu
  • Legit Hausa ta rahoto cewa wasu sabbin shugabannin jam'iyyar a gundumar Ganduje sun sake dakatar da Ganduje a ranar Lahadi
  • Amma da take mayar da martani, APC ta ce har yanzu dai aikin 'yan taware ne kuma za ta yi wa tufkar hanci nan gaba kadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta sake bayyana dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa a baya-bayan nan a matsayin aikin 'yan taware.

APC ta kuma kare Ganduje daga dakatarwar da aka yi masa karo na biyu a Kano
Kano: Jam'iyar APC ta ce za ta warware takaddamar dakatar da Ganduje nan gaba kadan. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Sakataren jam’iyyar a jihar Ibrahim Zakari Sarina ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Kano: Takaddama yayin da tsagin APC ya sake dakatar da Ganduje kan wasu sabbin dalillai

An dakatar da Ganduje karo na 2

Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu sabbin shugabannin jam’iyyar da suka fito daga gundumar Ganduje sun sake dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata ne muka ruwaito yadda wani tsagi na shugabannin jam’iyyar da ke gundumar ya dakatar da Ganduje.

A wannan sabuwar takaddamar, sakataren gundumar Ganduje, Ja'afar Adamu, a ranar Lahadi, ya ce halastattun shugabannin jam'iyyar su 11 ne suka dauki matakin.

Adamu ya ce shugabannin sun rattaba hannu kan takardar sabuwar dakatarwar da aka yi wa Ganduje, jaridar Premium Times ta ruwaito.

"Aikin 'yan taware ne" - Martanin APC

Amma da yake mayar da martani kan lamarin, Sarina ya ce har yanzu aikin 'yan taware ne wadanda ba halastattun shugabannin jam'iyyar bane na gundumar Ganduje.

Kara karanta wannan

Za a iya tsige Ganduje daga ofis kamar Oshiomhole? APC ta yi karin haske

Yayin da yake amincewa da wasu daga cikin shugabannin gundumar a matsayin ‘ya’yan jam’iyyar, ya ce ba su da mukami ko hurumi na daukar irin wannan matakin.

“Al’amari ne aikin 'yan taware har yanzu, kuma mun gano daukar nauyin su aka yi su aikata hakan a yammacin ranar Asabar."

- A cewar Sarina.

Sarina ya kara da cewa jam’iyyar a jihar na kokarin ganin ta gabatar da shugabannin jam’iyyar na gaskiya domin su warware wannan takaddama nan ba da jimawa ba.

Ganduje ba kamar Oshiomhole bane - APC

A wani labarin, jam'iyyar APC ta yi karin haske kan zargin da wasu ke yi na tunanin Abdullahi Ganduje na iya fuskantar dakatarwa kamar yadda aka dakatar da Adam Oshiomhole.

Sakataren yaɗa labarai na APC, Felix Morka ya ce Oshiomhole ya aikata laifi ne halastattun shugabannin jam'iyyar suka dakatar da shi, yayin da 'yan taware ne kawai ke kokarin dakatar da Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel