Dalilin da Ya Sa El-Rufai Ya Ziyarci Ofishin Jam’iyyar SDP, Jigon APC Ya Yi Bayani

Dalilin da Ya Sa El-Rufai Ya Ziyarci Ofishin Jam’iyyar SDP, Jigon APC Ya Yi Bayani

  • Jigon jam'iyyar APC, Dr. Ibrahim Modibbo ya bayyana dalilin da ya sa Nasiru El-Rufai ya kai ziyara ofishin jam'iyyar SDP da ke Abuja
  • A cewar Modibbo, El-Rufai ya fara sharar fagen tunkarar zaben 2027 kuma zai iya amfani da SDP wajen zama kalubake ga Bola Tinubu
  • Modibbo ya yi nuni da cewa, APC ta watsar da El-Rufai, wanda ya tilasta tsohon gwamnan Kaduna nema wa kansa mafita a harkar siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya kai ofishin jam'iyyar SDP ya jawo cece-kuce a tsakanin ƴan siyar Najeriya.

Na baya-bayan nan shi ne jigon jam'iyyar APC, Dr. Ibrahim Modibbo, wanda ya ce El-Rufai ya ziyarci SDP ne a shirye-shiryen shi na tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Hotunan Ribadu da jiga-jigan APC sun ziyarci El-Rufai yayin da ake jita-jitar zai bar jami'yyar

Jigon APC ya yi magana kan ziyarar El-Rufai ofishin jam'iyyar SDP
Dr. Ibrahim Modibbo ya ce El-Rufai ya ziyarci jam'iyyar SDP domin tunkarar zaben 2027. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Twitter

Modibbo wanda ya bayyana hakan ne a zantawarsa da talabijin na Arise, ya ce ziyarar El-Rufai wani mataki ne na yanke shawarar jam'iyyar da zai goya wa baya a 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"APC ta watsar da Nasir El-Rufai" - Modibbo

Jigon na jam'iyyar APC wanda kuma mai fashin baki ne a harkar siyasa, ya ce:

"Jam'iyyar APC ta watsar da Malam Nasiru El-Rufai, duk abin da take yi ba ta tuntubarsa, ina ga wannan ne dalilin da ya sa ya zaɓi ya nemi jam'iyyar da za ta dauke shi da muhimmanci.
"Kamar yadda Peter Obi ya yi a zaben 2023 da PDP ta hana shi takara, ya koma jam'iyyar Labour, kuma an ga yadda ya girgiza kasar, to kamar haka ne shi ma El-Rufai ya ke so ya yi."

"El-Rufai kwararre ne a siyasar Najeriya" - Modibbo

Kara karanta wannan

Cikin APC ya kada yayin da El-Rufa'i ya ziyarci babbar jam'iyyar adawa a Najeriya

Ko da aka tambaye shi yadda yake ganin tasirin Malam Nasiru El-Rufai a siyasar Najeriya, Modibbo ya ce:

"El-Rufai na daga cikin kwararru a harkar siyasar Najeriya. Mun ga irin namijin kokarin da ya yi a lokacin da ya ke ministan Abuja da kuma lokacin da ya ke gwamnan jihar Kaduna.
"Hatta rasa samun minista da ya yi ya samo asali ne daga irin tsarin siyasarsa na shugabanci, shi mutum ne mai tsaurin ra'ayi a kan tsare-tsaren mulki."

"El-Rufai zai girgiza siyasa a SDP" - Modibbo

Jigon jam'iyyar APC ya ci gaba da cewa Malam Nasiru El-Rufai, yana so ya yi amfani da jam'iyyar SDP domin tunkarar zaben 2027.

Ya ce tun bayan saukar El-Rufai daga gwamnan Kaduna aka daina jin duriyarsa, sai yanzu da ya dawo kasar ya fara ziyartar ƴan siyasa da jam'iyyu domin neman mafitarsa a zabe mai zuwa.

"Za mu iya cewa jam'iyyar SDP tana a doguwar suma, amma idan har El-Rufai ya shiga cikinta, zai farfaɗo da ita kuma ya girgiza siyasar Najeriya da ita."

Kara karanta wannan

Ramadan: Jerin jihohi 7 a Arewa da suka kashe N28.3b a shirin ciyar da al'umma abinci

A cewar Modibbo.

2027: El-Rufai na iya karawa da Tinubu?

Modibbo ya yi tsokaci kan tsare-tsaren jam'iyyar APC mai mulki, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya tafka kura-kurai da za su iya buɗewa El-Rufai kofar zama shugaban ƙasa a 2027.

Ya ce janye tallafin man fetur ba tare da samar da wani tsari na karin albashi, bunkasa rayuwar jama'a ba, ya jefa ƴan Najeriya a mawuyacin hali, wanda ya sa kowa ya dawo daga rakiyar APC.

"Idan har aka yi kuskuren Peter Obi ya hada kai da El-Rufai, to babu shakka za su iya samun nasara a zaben 2027. Duk da ana kallon El-Rufai na da tsattsauran ra'ayi, hakan ba zai hana a zabe shi ba."

A cewar Modibbo.

Kalli tattaunar a nan kasa:

Ribadu da kusoshin APC sun ziyarci El-Rufai

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ziyarci Nasiru El-Rufai.

Ribadu tare da wasu kusoshin jam'iyyar APC sun ziyarci El-Rufai jum kadan bayan da tsohon gwamnan Kaduna ya ziyarci jam'iyyar adawa ta SDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel