Hotunan Ribadu da Jiga-jigan APC Sun Ziyarci El-Rufai Yayin da Ake Jita-jitar Zai Bar Jami'yya

Hotunan Ribadu da Jiga-jigan APC Sun Ziyarci El-Rufai Yayin da Ake Jita-jitar Zai Bar Jami'yya

  • Yayin da ake ta jita-jitar cewa Nasiru El-Rufai zai bar jam'iyyar APC, tsohon gwamnan ya karbi manyan baki daga jam'iyyar a gidansa
  • Mai ba Shugaba Tinubu shawara a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da Kashim Ibrahim Imam na daga cikin wadanda suka ziyarci gidan nasa
  • Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya ziyarci ofishin jamiyyar SDP a birnin Abuja wanda ya saka shakku a zukatan mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya karbi bakuncin na hannun daman Shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Abuja.

Daga cikin wadanda ziyarci tsohon gwamnan akwai mai ba Tinubu shawara a harkokinsu tsaro, Nuhu Ribadu a yau Alhamis 21 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Cikin APC ya kada yayin da El-Rufa'i ya ziyarci babbar jam'iyyar adawa a Najeriya

An yada hotunan Nuhu Ribadu yayin ziyararsa ga El-Rufai
Nuhu Ribadu ya ziyarci Nasir El-Rufai a gidansa da ke Abuja. Hoto: Muyiwa Adekeye.
Asali: Twitter

Menene ake hasashe shi ne dalilin ziyarar?

Journalist KC ya wallafa hotunan jiga-jigan jami'yyar APC ciki har da Kashim Ibrahim Imam da sauransu da suka kai wa El-Rufai ziyara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ziyara na zuwa ne yayin da ake jita-jitar cewa tsohon Ministan na shirin watsar sa jam'iyyar APC mai mulki, cewar Intel Region.

Hakan ya biyo bayan ganin El-Rufai a ofishin jam'iyyar SDP ya kai musu ziyara a birnin Abuja.

El-Rufai ya ziyarci Fani-Kayode a gidansa

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ziyarci tsohon Ministan jiragen sama, Femi Fani-Kayode.

Bayan ziyarar, Fani-Kayode ya wallafa hotunansu tare a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Tsohon Ministan ya yabawa El-Rufai inda ya ce ya cika gwarzo a bangaren siyasa wanda ya shafe fiye da shekaru 20 ya na gwagwarmaya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Peter Obi ya halarci tafsirin Alkur'ani a babban masallacin Suleja

Bello El-Rufai ya magantu kan kujerar Minista

A baya, mun ruwaito muku cewa, Dan Majalisar Tarayya a jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya yi magana kan mahaifinsa, Nasiru El-Rufai game da kujerar Minista.

Bello ya ce El-Rufai ya ki amincewa da mukamin kujerar Minista sai da suka hadu suka roke shi kafin ya amince.

Sai dai ya ce ya ji bakin ciki yayin da Majalisar Dattawa ta ki amincewa da shi yayin da ake tantance Ministoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel