Ramadan: Jerin Jihohi 7 a Arewa da Suka Kashe N28.3b a Shirin Ciyar da Al’umma Abinci

Ramadan: Jerin Jihohi 7 a Arewa da Suka Kashe N28.3b a Shirin Ciyar da Al’umma Abinci

  • Akalla jihohin Najeriya bakwai ne suka fitar da sama da N28.3b domin gudanar da shirin ciyar da gajiyayyu a watan Ramadana na 1445
  • Wata kididdiga ta nuna cewa jihar Katsina ce ke kan gaba bayan da ta fitar da N10b domin aiwatar da shirin, sai jihar Yobe da ke ƙarshe
  • Sai dai malaman addini sun yi gargadin cewa akwai wadanda za su iya yin amfani da shirin wajen karkatar da dukiyar jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yayin da Ramadan ya kai kwana 10, jihohi bakwai na Najeriya sun fitar da sama da N28.3b domin ciyar da al'ummarsu abinci a watan azumin.

An kashe N28bn wajen ciyarwar Ramadan a Kano da wasu jihohi 6 a Ramadan
Ramadan: Jihohin Arewa 7 sun kashe N28bn wajen ciyarwa. Hoto: @dikko_radda, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Kamar yadda kididdigar jaridar Daily Trust ta nuna, jihohin sun hada da Katsina, Sokoto, Kano, Jigawa, Kebbi, Neja da Yobe.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

Ga bayanin kudin da jihohin suka kashe:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ramadan: Jihar Katsina ta fitar da N10b

Tashar Arise News ta ruwaito cewa gwamnatin jiihar Katsina ta ware Naira biliyan 10 domin gudanar da shirin ciyarwar.

Gwamna Dikko Radda, wanda ya sanar da yawan kudin ne a taron kaddamar da kwamitin rabon abincin, ya ce tallafin zai rage radadi ga al'umma.

2. Ramadan: Jihar Sokoto ta fitar da N6.7b

A jihar Sokoto kuwa, Gwamna Ahmed Aliyu ya ce jihar za ta kashe N6.7b a shirin ciyar da al'umma abinci a watan Ramadan.

Haka zalika, za a yi amfani da kudin wajen gudanar da rabon tallafin wasu kayayyakin ga mabukata da marasa galihu a jihar.

3. Ramadan: Jihar Kano ta fitar da N6b

Jihar Kano ce ke bi wa Sokoto, inda gwamnatin jihar ta ce za ta kashe N6bn domin ciyar da akalla mutane miliyan hudu a azumin bana.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya ware maƙudan kuɗi domin ciyar da mabuƙata a watan Ramadan

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Baba Dantiye ya bayyana hakan, yana mai cewa za ayi rabon ne a cibiyoyin dafa abinci da makarantun allo da masallatai.

4. Ramadan: Jihar Jigawa ta fitar da N2.83b

A jihar Jigawa kuwa, Sagir Musa, kwamishinan watsa labarai na jihar ya ce akwai cibiyoyi 608 da aka ware a fadin jihar da za su yi rabon abinci ga mutane 171,9000 kullum.

Musa ya ce an kuma bude wasu cibiyoyin a cikin kowace babbar makaranta a jihar, inda ake sa ran shirin zai amfani mutane miliyan 3.8 kafin azumin ya kare.

5. Ramadan:Jihar Kebbi ta ware N1.5b

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta ware N1.5b domin ciyar da talakawa da marasa galihu abinci a jihar, yayin da ta bude cibiyoyin ciyarwa 69.

An tsara cewa masallatai uku daga kowacce karamar hukuma ne za su gudanar da rabon abincin.

6. Ramadan: Jihar Neja ta fitar da N976m

Kara karanta wannan

Ramadan: Yadda Gidauniyar Dangote ke ciyar da Musulmai 10,000 a kullum a Kano

A jihar Neja, kwamishiniyar watsa labarai, Binta Mamman, ta ce gwamnati ta fitar da N976m domin ciyar da al'umma abinci a masarautu takwas na jihar.

Ta ce an sayo kayan abinci da za a rinka dafawa wanda aka raba wa kananan hukumomi 25, masarautu takwas, masallatai, jami'an tsaro da jam'iyyun siyasa a jihar.

7. Ramadan: Jihar Yobe ya fitar da N187m

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya amince da fitar da N187m domin gudanar da shirin ciyar da gajiyayyu a a jihar har zuwa kammala azumin bana.

Kamar sauran jihohi, ita ma jihar Yobe ta samar da cibiyoyin dafa abinci da rarraba su a yayin buda baki da sahur.

"A tabbatar an yi adalci" - Malamin addini

Mallam Ahmad Abdullahi, wanda ya zanta da Daily Trust, ya ce akwai bukatar shugabanni su ji tsoron Allah yayin da suka fitar da kudi domin ciyar da jama'a.

Kara karanta wannan

Ganduje ya dinke ɓarakar da ta kunno kai a APC, an sauya mataimakin dan takarar gwamna

Yayin da ya ke nuna muhimmancin ciyar da jama'a a watan Ramadan, Malam Abdullahi ya ce:

"Abu ne mai kyau, sai dai a Najeriya irin wannan abun akan samu matsala, wasu na amfani da hakan domin karkatar da kudi ko kayan abincin, wasu kuma abincin ba zai iya ciyuwa ba."

Ramadan: Matashi ya faranta ran mahaifiyarsa

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo rahoton wani matashi da ya aika wa mahaifiyarsa kudi domin ta yi hidimar azumi.

Jim kadan da aika mata da kudin, mahaifiyar ta biyo shi ta WhatsApp, tayi masa ruwan addu'o'i tare da fatan nasararsa a rayuwa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na TikTok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel