Ramadan: Peter Obi Ya Halarci Tafsirin Alkur’ani a Babban Masallacin Suleja

Ramadan: Peter Obi Ya Halarci Tafsirin Alkur’ani a Babban Masallacin Suleja

  • Peter Gregory Obi na kara na ci gaba da himmatuwa wajen gudanar da ayyukan azumin Ramadan tare da Musulmai a fadin Najeriya
  • An hangi dan takarar jam'iyyar Labour ya halarci taron ibada a babban masallacin Suleja dake kan titin Suleja-Kaduna a jihar Neja
  • Tare da sauran masu ibada, Obi ya saurari tafsirin Alkur'ani da limamin masallacin ya gabatar a ranar Talata 19 ga Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Neja - An sake ganin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi a yana ayyukan azumi a tare da musulmi.

Peter Obi wajen taron tafsirin Al-Kur'ani a Neja
Ramadan: Peter Obi ya ziyarci babban masallacin Suleja. Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Peter Obi ya saurari tafsirin Al-Kur'ani

A ranar Talata, 19 ga watan Maris aka gano tsohon gwamnan jihar Anambra a babban masallacin Suleja da ke kan hanyar Suleja zuwa Kaduna a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ganshi yana zaune a sahun gaba cikin daruruwan musulmi, yana sauraren tafsirin Al-Kur'ani da limamin masallacin yake gabatarwa.

Wani ma'abocin dandalin X, @Imranmuhdz, ya wallafa bidiyon dan siyasar a lokacin da yake zaune a masallacin.

Kalli bidiyon a kasa:

Peter Obi: Abin da mutane ke cewa

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan bidiyo na Peter Obi kamar haka:

@OgaBossTweets ya ce:

"Wannan neman suna ne da siyasa kawai.
"Lallai wannan shi ne wasan wasa."

@MA_Dibola ya ce:

"Abin da ya rage masa shi ne ya tafi wajen bautar dodanni."

@Fifa737 ya ce:

"Idan Tinubu ne yake yin haka, za ku ce ba komai, amma idan Obi ne, sai kuce siyasa ce. Jama'a kar ku manta cewa dukkansu 'yan siyasa ne. Eh wannan yunkuri ne na siyasa, to ku bar shi a haka kawai."

Kara karanta wannan

Ramadan: Matakin da ƴan sandan Kano suka ɗauka kan wasannin 'tashe'

@Abdul_charming ce:

"Amma abin da yake yi bai yi yawa ba kuwa?"

@AliyuSharif ce:

"Ni fa na fara zargin wani abu."

@plutoboy1990 ce:

"Wannan shi ne abin da ya kamata ace ka yi a lokacin yakin neman zabe."

Peter Obi ya je masallacin Nyanya-Maraba

A wani labarin makamancin wannan, wani faifan bidiyo ya nuna Peter Obi a babban masallacin Nyanya-Maraba, inda ya ci abinci tare da musulmi a lokacin buda baki.

Legit Hausa ta ruwaito cewa dan siyasar ya zauna a kasa yana ba wani yaro abincin a baki yayin da shima yake ci, lamarin da ya jawo cece-kuce a dandalin X.

Asali: Legit.ng

Online view pixel