Zaben 2027: APC Ta Yi Martani Yayin da Atiku Ya Fara Tunanin Takarar Shugaban Kasa

Zaben 2027: APC Ta Yi Martani Yayin da Atiku Ya Fara Tunanin Takarar Shugaban Kasa

  • Jam’iyyar APC ta shawarci Alhaji Atiku Abubakar da ya bar siyasa ya manta da neman mulki kwata-kwata
  • Jam’iyyar APC ta bayyana cewa wasu muƙarrabansa da abokan siyasa suna yaudarar Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar PDP
  • Jam'iyyar mai mulki tana mayar da martani ne kan wata fallasa da sansanin Atiku ya yi na cewa zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da shirin da aka bayyana na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023, Atiku Abubakar, na tsayawa takara a zaɓen 2027.

Daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, a wata hira da jaridar The Punch, wacce aka buga a safiyar Alhamis, 4 ga watan Janairu, ya bayyana burin Atiku na 2027 a matsayin labarai mafi ban dariya na 2024.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya yi hasashen matsala ga PDP, ya bayyana babban gwammnanta da zai koma APC

APC ta yi wa Atiku martani
Atiku Abubakar na da burin zama shugaban ƙasa Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

2027: APC ta ce Atiku ba barazana ba ne

Atiku Abubakar mai shekara 77 a duniya, ya yi takarar shugabancin Najeriya sau shida bai yi nasara ba, a 1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim yace Atiku zai faɗi zaɓen shugaban ƙasa a 2027 da babban kaye. A cewarsa, za a sake kayar da jigon na PDP.

A kalamansa:

"Jam’iyyarmu wacce ita ce APC, ta kayar da Atiku ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Ko da a lokacin da muka yi tunanin yana da kuzari da kuma ƴar nagartar da za ta sanya ƴan Najeriya su zaɓe shi, mun kayar da shi gaba ɗaya.
"Ta yaya wanda kawai yake ƙoƙarin dawo da martabarsa zai iya zama barazana ga APC a 2027? Wannan ba abun da zai faru ba ne. Atiku ba zai taɓa zama barazana ga APC ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna kuma Sanata ya watsar da jam'iyyarsa zuwa APC, ya bayyana manyan dalilai

"Bai kasance barazana ba lokacin da yake da ƴar ƙaramar ƙima. Ta yaya zai zama barazana bayan ya riga ya zama marar amfani? Mafarki ne da ba zai faru ba."

APC ta ce an daina yayin Atiku

Jigon na APC ya ƙara da cewa:

"Atiku ba wani wanda za a dama da shi bane, bai taɓa zama wanda za a dama da shi ba, kuma ba zai iya zama a 2027 ba lokacin da ƙimarsa ta siyasa ta gama ƙarewa."

Jam'iyyar PDP Ta Magantu Kan Korar Shugabanta

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar PDP, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar na jihar Ondo.

Kwamitin ya bayyana cewa dakatarwar ta saɓa wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar, inda ya yi barazanar ɗaukar mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel