Ka tsufa, Hakura da Zancen Takarar 2027 – Tsohon shugaban PDP ga Atiku Abubakar

Ka tsufa, Hakura da Zancen Takarar 2027 – Tsohon shugaban PDP ga Atiku Abubakar

  • Olabode George bai goyon bayan Atiku Abubakar ya fito neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP
  • ‘Dan siyasar ya ce a 2027, Wazirin Adamawa ya yi tsufa da tsayawa takara ko ya mulki ‘yan Najeriya
  • George yana so a bar mutanen Kudu su shafe shekaru takwas a mulki yadda Arewa ta samu damarta

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Olabode George yana ganin babu dalilin da Atiku Abubakar zai sake neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasar yana ganin shekaru sun kama Atiku Abubakar, Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da Bode George Hoto: Atiku Abubakar/arise.tv
Asali: Facebook

2027: Atiku Abubakar ya tsufa?

Ko Wazirin Adamawa ya yi nasara a takarar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa, Bode George yana ganin bai da kuruciyar mulki.

Kara karanta wannan

Na hannun daman Atiku ya sake sanya labule da Tinubu a Paris, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar ya yi wannan magana ne a ofishinsa da ke Legas da ya zanta da ‘yan jarida, dama can bai goyi bayan Atiku a 2023 ba.

Bode George yana yi wa Atiku Abubakar kallon uba a jam’iyyar adawar, yake cewa a 2027 kamata ya yi ya horas da wani mai jini a jika.

Idan Atiku ya fito neman mulkin Najeriya nan da shekaru uku, zai kasance shekara 81. 'Dan siyasar ya nemi takara sau shida a tarihi.

George yana so PDP ta kai takara Kudu

An rahoto George yana cewa PDP ba za ta biyewa ‘yan adawa wajen shiga wata babbar jam’iyya hamayya da ake hari a zabe mai zuwa.

A ra’ayin tsohon shugaban na PDP, ya kamata jam’iyyarsu ta kebe takarar shugaban kasa a 2027 ta yadda za a tsaida mutumin kudu ne.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci game da alakarsa da su Kwankwaso

Wasu suna ganin yanzu lokacin kudancin kasar ne a kan mulki har zuwa 2031.

Bode George a kan batun tsaro

Nigerian Lawyer tace George ya ce lamarin tsaro ya zama abin takaici, yana neman dabbaka matsayar taron CONFAB da aka yi a 2014.

A bangaren tsaron, ‘dan siyasar ya ba Bola Tinubu shawara ya tara tsofaffin janarorin soja domin su ba shi shawarar yadda za a samu sauki.

Atiku zai samu tikitin PDP?

Kwanaki rahoto ya zo cewa Bode George ya gargadi jiga-jigan PDP cewa daga Kudu za a fito da ‘dan takaran shugaban kasa a zaben 2027.

Idan ta George ne sai a 2031 jam'iyyar hamayyar za ta koma Arewa ta bada tuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel