Kano: Ganduje Ya Tafka Asara Bayan Ciyamomi 3 Sun Watse Masa Tare da Komawa NNPP, Abba Ya Karbe Su

Kano: Ganduje Ya Tafka Asara Bayan Ciyamomi 3 Sun Watse Masa Tare da Komawa NNPP, Abba Ya Karbe Su

  • Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya sake rasa dama a Kano bayan wasu ciyamomi sun sauya sheka
  • Akalla ciyamomi uku ne a jihar suka sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a jihar, NNPP inda Gwamna Abba ya karbe su
  • Kananan hukumomin sun hada da Dawakin Tofa da Garun-Malam da kuma karamar hukumar Nassarawa da ke jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar APC a jihar Kano ta tafka mummunar asara bayan ciyamomin kananan hukumomi uku sun watse mata.

Ciyamomin sun sauya sheka ne zuwa jam'iyya mai mulki a jihar, NNPP inda Gwamna Abba Yaushe suka sauya shekar a KanoKabir ya karbe su.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisar Tarayya a NNPP ya gwangwaje 'yan jam'iyyarsa da abin alkairi, ya fadi dalili

APC ta yi asara bayan ciyamomi 3 sun sauya sheka a Kano
Ciyamomin kananan hukumomi 3 sun sauya sheka zuwa NNPP. Hoto: Umar Ganduje, Abba Kabir.
Asali: Facebook

Yaushe suka sauya shekar a Kano?

Wadanda suka sauya shekar sun hada Ado Tambai Kwa na karamar hukumar Dawakin Tofa inda nan ne mazabar Abdullahi Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da ciyaman din karamar hukumar Nassarawa, Auwalu Lawan Aramposu sai Mudassiru Aliyu na Garun-Malam.

Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa ya sauya shekar ce da mataimakinsa, Garba Yahaya Labour da wasu kansiloli.

Yayin karbar su a gidan gwamnatin jihar, Gwamna Abba Kabir ya yaba musu kan wannan mataki da suka dauka, cewar Kano Focus.

Abba ya ba su tabbacin daidaito da sauran 'yan jam'iyyar ba tare da wani bambanci ba inda ya ce NNPP gidan kowa ne.

Martanin Gwamna Abba Kabir a Kano

Ya ce:

"Za mu yi aiki tare da kowa wanda zai kasance da mu don ciyar da jihar Kano gaba, kuma za mu yi haka ne don Kano.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon APC ya gaji da tsarin Tinubu, ya nemi a sake zama kan tsare-tsaren gwamnati

"Mun yi sa'a wasu daga cikinku sun gane irin tsarin shugabancinmu tare da yanke hukuncin dawowa don a tafi tare don jihar Kano, muna muku maraba."

Wannan sauya shekar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Ganduje ya yi kira ga 'yan jam'iyyar NNPP su dawo jam'iyyar APC.

Kwankwaso ya yabawa Tinubu

Kun ji cewa, jigon APC a Kano, Ilyasu Kwankwaso ya yabawa Tinubu kan matakin fitar da abinci.

Kwankwaso ya ce wannan mataki zai rage halin matsin da ake ciki bayan cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel