Zaben Cike Gurbi: Jam'iyyar NNPP Ta Lallasa APC a Mazabu 2 a Kano, Bayanai Sun Fito

Zaben Cike Gurbi: Jam'iyyar NNPP Ta Lallasa APC a Mazabu 2 a Kano, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbi da aka yi a wasu mazaɓu a jihar Kano
  • Hukumar ta sanar da ɗan takarar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen a mazaɓar Kura/Garun Mallam ta majalisar dokokin jihar
  • Hakazalika a mazaɓar Rimin Gado/Tofa ɗan takarar NNPP ya lallasa takwaransa na jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Alhassan Ishaq na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi ranar Asabar a mazaɓar Kura/Garun Mallam ta majalisar dokokin jihar Kano.

Baturen zaɓen Farfesa Shehu Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 37,262 inda ya doke Musa Daurawar na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 30,803, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

INEC ta dakatar da zaɓen cike gurbin da ake yi a Kano da wasu jihohi 2, ta jero dalilai

NNPP ta lallasa APC a Kano
Jam'iyyar NNPP ta lashe zabe a mazabu biyu na Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Tun da farko dai kotun ɗaukaka ƙara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe 20 da ke mazaɓar Kura/Garun Malam a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta lallasa APC a Kano

Hakazalika, INEC ta bayyana Bello Butu-Butu na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na ranar Asabar a mazaɓar Rimin Gado/Tofa.

Baturen zaɓen Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya kuma bayyana cewa Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 31,135 inda ya doke abokin hamayyarsa na APC wanda ya samu ƙuri’u 25,577.

An dai gudanar da zaɓen ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zaɓe 33 a mazaɓar Rimin Gado/Tofa.

APC Ta Lashe Zaɓen Maye Gurbin Gbajabiamila

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC ta sanar da wanda ya yi nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Legas, domin maye gurbin Femi Gbajabiamila.

Hukumar ta bayyana Fuad Laguda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazabar Surulere a majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel