Kano: Sanusi II Ya Soki APC a Maganar Farko a Fili Bayan Nasarar Abba a Kotun Koli

Kano: Sanusi II Ya Soki APC a Maganar Farko a Fili Bayan Nasarar Abba a Kotun Koli

  • Muhammadu Sanusi II ya ce APC ta makara wajen karbar kaddara a zaben gwamnan jihar Kano
  • Sarkin Kano na 14 ya yi jawabi yana taya al’ummar jihar Kano murnar abin da ya faru a kotun koli
  • Sanusi II yake cewa alkalan kotun koli sun tabattar da zabin Kanawa a 2023, Abba Kabir Yusuf

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Mai martaba Muhammadu Sanusi II, ya yi tsokaci biyo bayan kammala shari’ar zaben gwamnan Kano da aka yi a 2023.

A wani jawabin bidiyo da Legit ta samu a dandalin X, Muhammadu Sanusi II ya taya al’ummar kasar Kano nasarar abin da ya faru.

Muhammadu Sanusi II
Muhammadu Sanusi II da Nasiru Gawuna Hoto: @MSII_dynasty, Muneer A. Sidi
Asali: Facebook

Ranar Juma’a da ta gabata, kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a kan mulki.

Kara karanta wannan

Mutane 6 da Suka Taimakawa Abba Kabir Yusuf Wajen Samun Nasarar Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Sanusi II ya ce a yi wa Kano adalci

Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ce a baya sun yi jan-kunne da kuma kira ga alkalan kotun koli su yi wa al’umma adalci.

Da taimakon Madakakin Sarki Allah SWT, mai Martaban ya ce Kanawa sun tsira da abin mafi yawansu su ka zaba a takarar 2023.

"A bar mutane da zabinsu" - Sanusi II

“Abin da muke fada a ko da yaushe tun da an ce mulkin farar hula ake yi ba mulkin mallaka ba, al’umma suke da hakkin zaben shugabanninsu da wakilansu
Idan sun zaba, an tabbatar ga wanda suka zaba, an hana su to zalunci ne, ba wanda aka zaba aka zalunta ba, al’ummar da su ka jefa kuri’a aka yi wa kwace hakkinsu.

- Muhammadu Sanusi II

Khalifa Sanusi II ya yi tir da zalunci

Kara karanta wannan

Abba ya nunawa duniya masoyansa a Kano da ya dawo bayan hukuncin Kotun Koli

Khalifan Tijjaniyan a Najeriya ya yi gargadi cewa Ubangiji Allah ba zai bari a zalunci jama’a ba, ya ce abin da ya faru babban darasi ne.

A bidiyon da aka wallafa a shafin X da sunan Mai martaba, Sanusi II ya ce amfani da alkalai a karbe gwamnati ba tsarin farar hula ba ne.

Sarkin Kano na 14 ya yi magana a kan tawakkali, dogara da kaddara da kuma karbar hukuncin Allah Sarki SWT a matsayin musulmai.

Yaushe ne lokacin tawakkali a musulunci?

Khalifa yake cewa an yi zabe kuma an dankara wasu da kasa, sun garzaya kotu inda aka yi galaba a kan su bayan kokarin fisge mulki.

Mai martaba Sanusi II ya ce a kotun koli ne aka takawa APC burki, sai kuma suka dawo suna cewa sun rungumi kaddarar ubangiji.

Lokacin da aka yi zabe kuma NNPP tayi nasara ya dace 'yan APC su karbi kaddara, ba bayan alkalami ya bushe a kotun karshe ba.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya warware abin da Ganduje ya so a shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

Abba ya dawo Kano a ranar Lahadi

Kuna da labarin yadda Abba Kabir Yusuf ya yi awanni fiye da 12 a kan hanya kafin ya isa gidan gwamnati daga Kaduna a ranar Lahadi.

‘Yan Kwankwasiyya sun rika rawa da waka, suna maraba da ‘Mai Rusau’ da Abba ya dawo Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel