Ganduje: Mutanen da su ka sa muka kirkiro sababbin masarautu a Kano a 2019

Ganduje: Mutanen da su ka sa muka kirkiro sababbin masarautu a Kano a 2019

- Abdullahi Umar Ganduje ya fadi dalilin kara yawan Sarakunan da ke Kano

- Gwamnan ya ce Malamai da sauran jama’a ne suka roki a kara masarautun

- Ganduje ya ke cewa gwamnatinsa ta share hawayen masu yin wannan kira

A ranar Asabar ne, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi bayani game da abin da ya sa gwamnatinsa ta kara yawan masarautu.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya kara ya kara masarautu hudu a jihar Kano ne saboda mutane sun nuna suna da bukatar hakan.

Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa dukkan wasu bangarorin wasu mutane a jihar Kano sun nemi wannan alfaramar.

KU KARANTA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi alheri ne - 'Yan Tijjaniya

Jaridar The Nation ta rahoto gwamnan ya na cewa shawarar mutane ta sa aka dauki wannan matsayi.

Ya ce: “Mutane da dama sun taru suka sa aka cin ma wannan matsaya na kara yawan masarautun jihar. Wadannan masu ruwa da tsaki sun taimaka ta hanyoyi dabam-dabam wajen kafa sababbin masarautun, a ka kai ga matsayin da ake ciki.”

Mai girma Ganduje ya yi wannan bayani ne a lokacin da Mai martaba Sarkin Rano, Muhammad Kabir Inuwa, ya kawo masa ziyarar sallah a gidan gwamnati.

“Daga bangarenmu, a matsayinmu na gwamnati, mun amsa kira da koken da mutanenmu su ke yi. Mun yi bakin kokarinmu na ganin mun yi abin da ake bukata.”

Ganduje: Mutanen da su ka sa muka kirkiro sababbin masarautu a Kano a 2019
Abdullahi Ganduje Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mahaifiyar sarkin Kano da Rano, Maryam Bayero, ta rasu

“Malamai da shugabannin al’umma suka yi ta rokon a kara masarautu. ‘Yan kasuwa suka bi sahu. Kungiyoyin dalibai da matasa da mata suka dage a kan wannan.”

Gwamnan ya ambato amfanin kara masarautun, ya ce ya sa ana titin da ya hada garuruwan Karfi, Bunkure, Rano, Kibiya, Burum-Burum, Sumaila, da Kwanar Sumaila.

Haka zalika gwamnan ya ce yanzu za a fadada babban asibitin garin Rano, ta yadda za a samu gadaje 400.

Kafin Dr. Abdullahi Ganduje ya hau mulki, sarki daya ake da shi a jihar Kano, a shekarar 2019 ne ya kirkiro masarautu a kasashen Bichi, Karaye, Rano da Gaya.

Gwamnan jihar Kano ya ce ‘yan majalisar dokoki sun bi duk wasu ka’idoji da suka dace wajen ganin an kawo dokokin da su ka kafa sababbin masarautun hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel