Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Taka Rawa a Hukuncin Kotun Koli na Zaben Gwamnonin Kano da Plateau

Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Taka Rawa a Hukuncin Kotun Koli na Zaben Gwamnonin Kano da Plateau

  • Kotun Ƙoli a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, ta yanke wasu muhimman hukunce-hukuncen da suka tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Caleb Mutfwang
  • Kotun Ƙolin ta yi watsi da ƙararrakin da aka shigar na neman soke nasarar da suka samu a zaɓen da aka gudanar a jihohin na ranar 18 ga watan Maris
  • Da yake magana da Legit.ng, Williams Dakwom, jigo a jam’iyyar APC, ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu ya shawarci alkalan Kotun Ƙoli domin hana tada zaune tsaye

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Williams Dakwom, ya mayar da martani kan hukuncin Kotun Ƙoli da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya bayyana dalili 1 da ya hana Tinubu kin tsoma baki a shari'ar zaben gwamnan Kano

Idan ba a manta ba a ranar Juma’a 12 ga watan Janairu ne Kotun Ƙoli ta bayyana cewa kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara sun yi kuskure wajen korar Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.

Jigon APC ya yi magana kan hukuncin Kotun Koli
Jigon APC ya fadi rawar da Tinubu ya taka a shari'ar zaben gwamnonin Kano da Plateau Hoto: Caleb Mutfwang, Abba Kabir Yusuf
Asali: UGC

Daga nan ne Kotun Ƙolin ta yi watsi da hukuncin da kotunan biyu suka yanke tare da tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, Kotun Koli ta sauya korar Caleb Mutfwang, inda ta tabbatar da shi a matsayin gwamnan jihar Plateau.

Wacce rawa Shugaba Tinubu ya taka?

Da yake mayar da martani a wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu ta wayar tarho, Dakwom ya ce alƙalan Kotun Ƙoli sun yi biyayya ga umarnin shugaban ƙasa.

Dakwom ya yi iƙirarin cewa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shi ne na a kaucewa hargitsi da kuma tabbatar da cewa kowane ɗan takara ya samu nasararsa, inda ya yi nuni da wani yunƙurin siyasa na son samun jam’iyya ɗaya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya cimma yarjejeniya da Tinubu kan shari'ar zaben gwamnan Kano? Gaskiya ta bayyana

Jigon na jam’iyyar ta APC ya kuma nuna cewa shawarar da shugaban ƙasa ya ba alƙalan wata dabara ce domin zaɓen 2027 mai zuwa, inda yake hasashen yin takara ba tare da samun abokan hamayya ba.

'Shugaba Tinubu na son zaman lafiya', Dakwom

Dakwom ya bayyana cewa:

"Gwamnonin Kano, Plateu da Zamfara sun yi nasara ne saboda shugaban ƙasa ya bayar da shawarar cewa ba ya son tayar da zaune tsaye.
"Shirin da aka yi shi ne a haifar da hargitsi a cikin ƙasa amma shugaban ƙasa ya ba da shawarar a ba kowa nasararsa.
"Daga yadda shugaban ƙasa yake tafiya, yana son tsarin jam'iyya ɗaya ne kuma yana son yanayin da a 2027 babu wanda zai tsaya takara da shi."

Mutfwang Ya Magantu Kan Nasararsa

A wani labatin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi magana kan hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya tabbatar da nasararsa.

Gwamnan ya nuna farin cikinsa kan hukuncin inda ya nuna cewa ƙasar nan ta kama hanyar daidaituwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel