Jerin Sunaye: Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Sarakuna 6 a Jiharsa, Ya Ƙara Wa Wasu 11 Girma

Jerin Sunaye: Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Sarakuna 6 a Jiharsa, Ya Ƙara Wa Wasu 11 Girma

  • Gwamna Ademola Adeleke ya naɗa sabbin sarakuna shida kuma ya ɗaga darajar wasu guda 11 a jihar Osun
  • Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Kolapo Alimi, ne ya tabbatar da haka bayan taron majalisar zartarwa ranar Talata
  • Ya bayyana cewa naɗin da karin girman zai fara aiki ne nan take kuma ya jero sunayen waɗanda lamarin ya shafa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta amince da nadin sabbin sarakunan gargajiya guda shida domin cike gurabe a masarautun yankunan su.

Karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke, Gwamnatin Osun ta aminta da naɗin ne a taron majalisar zartarwa ta jihar wanda ya gudana ranar Talata.

Kara karanta wannan

Miyagu sun harbe babban limamin Masallacin Jumu'a da ɗan acaɓa a Filato

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun.
Gwamnatin Osun Ta Nada Sabbin Sarakuna Shida, Ta Kara Ma Wasu Matsayi Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Sabbin sarakunan da aka naɗa sun haɗa da Yarima Adekunle Waheed a matsayin Eleko na Eko-Ende, Yarima Haastrup Adeola a matsayin Aloro na Iloro-Ijesha, da Yarima Mark Adeniyi a kujerar Onise na Ise-Ijesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune, Yarima Sulaimon Adebayo a matsayin Olu na Alajue, Yarima Badmos Rafiu a matsayin Alagbeye na Agbeye, da kuma Yarima Johnson Oyewale, Olola na Ola.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar kan al'umma na jihar Osun, Kolapo Alimi, ya fitar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Adeleke ya ɗaga darajar wasu sarakuna 11

Ya kara da cewa an daukaka darajar wasu sarakunan gargajiya goma sha daya zuwa matakin sashe na II, wanda doka ta amince da shi a Cap 25, na kundin dokokin Jihar Osun, 2002.

Sanarwan ta ƙara da cewa:

"Sarakunan da aka ɗaga darajarsu sun haɗa da, Olu Ilu Oba Oyeyemi, Alayetoro na Ayetoro Ijesa, Onikajola na Kajola Bowaje-Ijesa, Olorogoji na Orogoji-Ijesa, Onimelu na Ifemelu -Ifewara da Alarunde na Arunde Ifewara."

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dokokin jihar PDP ya yi murabus daga muƙaminsa, ya ajiye kujerar gaba ɗaya

"Sauran sune, Olu na Araromi-Owu; Olu na Akiriboto-Isale da kuma Onijimo na Ijimo-Ijesha. Matakin zai fara aiki ne nan take."

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta janye daga yunkurin naɗa Sarkin Masarautar Koka, inda ta ba da umarnin gudanar da bincike tare da gyara wasu kura-kurai da rashin bin ka’ida wajen zaben.

Abba Kabir ya rantsar da sabbin hadimai a Kano

A wani rahoton na daban Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shaida bikin rantsar da manyan sakatarori 11 tare da sabbin masu bada shawara ta musamman 14.

Ya yi wannan ne yayin da ake ci gaba da dakon zaman karshe na yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano a kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel