Na Cancanci Zama Shugaban Kasa, Gwamnan PDP Ya Bayyana Kwadayinsa Kan Kujerar, Ya Fadi Dalili

Na Cancanci Zama Shugaban Kasa, Gwamnan PDP Ya Bayyana Kwadayinsa Kan Kujerar, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya magantu kan neman shugabancin kasar Najeriya inda ya ce ya na da kwarewa
  • Adeleke ya bayyana cewa ya na da dukkan abin da ake bukata kuma ya cancanci kujerar inda ya ce zai yi amfani da wannan damar
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke hira da gidan talabijin na Arise a yau Juma'a 29 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana aniyarsa ta kwadayin neman shugabancin Najeriya.

Adeleke ya ce ya tabbatar ya cancanci kujerar shugabancin kasar inda ya ce da zarar ya samu dama ba zai bar ta ba.

Kara karanta wannan

Akeredolu: Tinubu ya girgiza da mutuwar gwamnan Ondo, ya tura sako ga gwamna mai jiran gado

Gwamnan PDP ya kwadaiu da kujerar shugabancin Najeriya
Gwamna Adeleke na jihar Osun ya kwadaitu da kujerar shugaban kasa. Hoto: Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Mene Adeleke ke cewa kan kujerar shugaban kasa?

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke hira da gidan talabijin na Arise a yau Juma'a 29 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ademola ya ce ya na da kyakkyawar alaka da shugaban kasa, Bola Tinubu inda ya ce a kullum ya na masa fatan alkairi.

A cewarsa:

"Na cancanci zama shugaban kasar Najeriya, me yasa ba zan karba ba idan Ubangiji ya kawo lokacin?."

Mene gwamnan ke cewa kan Shugaba Tinubu?

"Zan yi amfani da wannan damar don kyautatawa al'umma ta, ba zan iya cewa a'a ba komai na iya faruwa.
"Ina da kyakkyawar alaka da Shugaba Tinubu wanda na ke masa fatan alkairi da kuma samun karin lafiya."

Adeleke ya kuma bayyana irin ayyukan alkairi da ya ke yi a jiharsa duk da gadar tarin basuka da ya yi a lalitar jihar, Naija News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Za mu shawo kan dukkan matsaloli tare da karfafa Najeriya - Ganduje

Ya ce akalla ya samu tulin basukan fiye da naira biliyan 40 inda ya ce hakan ya jawo masa matsala a kokarin biyan albashin ma'aikata.

Adeleke ya bayyana burinsa kafin zama gwamna

A wani labarin, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana babban burinsa a rayuwa kafin zama gwamnan jihar.

Adeleke ya ce babban burinsa shi ne zama mawaki kamar yadda ɗansa, Davido ya kasance shahararren mawaki a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel