Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Ajiye Kujerar Gaba Ɗaya

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Ajiye Kujerar Gaba Ɗaya

  • Shugaban majalisar dokokin jihar Ribas na tsagin Gwamna Fubara, Edision Ehie, ya yi murabus daga muƙaminsa, ya aje kujerar ɗan majalisa
  • Honorabul Ehie ya aike da wasiƙa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) amma bai ambaci dalilin yin murabus ɗin ba
  • Ana hasashen hakan ba zai rasa nasaba da sulhun da aka yi a fadar shugaban ƙasa tsakanin Gwamna da Nyesom Wike ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsagin Gwamna Similanayi Fubara, Honorabul, Edision Ehie ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban majalisar.

Honorabul Ehie ya kuma aje kujerarsa ta mamba mai wakiltar mazaɓar Ahaoda ta gabas 2 a zauren majalisar dokokin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Honorabule Ehie ya yi murabus.
Kakakin Majalisar Dokoki Da Ke Goyon Bayan Fubara Ya Yi Murabus Hoto: Edision Ehie
Asali: Facebook

Ya tabbatar da ɗaukar waɗannan matakan ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 29 ga watan Disamba, 2023 da kuma adireshin hukumar zaɓe (INEC), The Angle ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ya ɗauki wannan matakin?

Sai dai tsohon ɗan majalisar bai bayyana maƙasudin da ya sa ya aje muƙaminsa kuma ya aje kujerarsa ta mamban majalisar dokokin jihar Ribas ba a cikin wasiƙar.

Amma ya godewa takwarorinsa na majalisar bisa kyakkyawar alakar da suka yi tare, kana ya gode wa mutanen mazaɓarsa bisa goyon bayan da suka ba shi na tsawon lokacin da ya shafe a majalisar.

Mista Ehie shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ribas ta 10 har zuwa lokacin da aka dakatar da shi bayan rushewar yunkurin tsige Gwamna Fubara.

Jim kaɗan bayan dakatar da shi ne kuma ya ɓalle, ya ayyana kansa a matsayin shugaban majalisar dokokin yayin da ƴan majalisa 4 ne kacal a tsaginsa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya faɗi matsala 1 da ke neman rusa lissafin APC gabanin hukuncin kotun kolin Najeriya

Gwamna Similanayi Fubara ya gabatar da kudirin kasafin kudin jihar na shekarar 2024 ga mambobin majalisar hudu karkashin jagorancin Ehie, mai biyayya gare shi.

Ana ganin murabus din Ehie ba zai rasa nasaba da yarjejeniya 8 da suka cimma da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ba a wani taron sulhu da aka yi kwanan nan a Villa, Abuja.

‘Yan Majalisa Za Su Kashe Naira Biliyan 344 a Kan Abubuwa 29

A wani rahoton kuma Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilan tarayya za su iya batar da abin da ya zarce N300bn a shekarar nan ta 2024.

‘Yan majalisar sun yi kari a cikin kasafin kudinsu, za a jira amincewa da sa hannun Mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel