Awanni Kadan Bayan Shiga Ofis, Sabon Gwamna Lucky Ya Nada Mukamai, Ya Yi Wani Gagarumin Abu 1

Awanni Kadan Bayan Shiga Ofis, Sabon Gwamna Lucky Ya Nada Mukamai, Ya Yi Wani Gagarumin Abu 1

  • Sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya nada sabbin mukamai awanni kadan bayan hawa karagar mulki
  • Aiyedatiwa ya nada Ebenezer Adeniyan a matsayin sakataren yada labaransa da wasu mutane hudu mukamai daban-daban
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ma'aikatan jihar, Omojuwa Olusegun ya fitar a yau Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Awanni kadan bayan hawa karagar mulki, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya nada sabon mukami.

Sabon gwamnan jihar Ondo ya nada Ebenezer Adeniyan a matsayin sakataren yada labaransa, cewar The Nation.

Sabon gwamnan Ondo ya yi sabbin nade-nade
Sabon Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Ya Nada Mukamai. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Yaushe sabon gwamnan ya yi nade-naden?

An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ma'aikata, Omojuwa Olusegun ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun ya ce sauran mukaman sun hada da Smart Omodunbi Jnr a matsayin hadiminsa a bangaren siyasa sai Abire Sunday Olugbenga hadimi a bangaren yada labarai na zamani.

Sauran sun hada da Motunrayo Oyedele hadima a bangaren daukar hoto sai Dakta Temitayo Iperepolu hadimi a bangaren aikace-aikacen, cewar Vanguard.

Wane mataki kuma sabon gwamnan ya dauka?

Gwamnan ya kuma ayyana kwanaki uku don hutu da kuma yin jimamin rasuwar tsohon gwamnan.

Ya kuma bukaci a saukar da tutuci kasa don nuna alhini kan rasuwar gwamnan a jihar da ya rasu a yau Laraba.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a yau Laraba 27 ga watan Disamba a kasar Jamus.

Daga bisani, an rantsar da Lucky a matsayin sabon gwamnan jihar da yammacin yau Laraba a jihar da misalin karfe hudu na yamma.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: An rantsar da sabon gwamnan Ondo bayan mutuwar Gwamna Akeredolu, bayanai sun fito

Lucy Aiyedatiwa ya zama gwamnan Ondo

A wani labarin, A yau Laraba ce 27 ga watan Disamba aka rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa.

Lucky ya zama gwamnan ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a yau Laraba bayan ya sha fama da jinya a kasar Jamus.

Wannan rahoto ya jero muku wasu muhimman abubuwa guda biyar game da sabon gwamnan da ya kama aiki a yau Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel