Tsohon Ministan Buhari Ya Ci Gyaran Shugaba Tinubu a Kan Abubuwa 2 da Ya Aikata a Ofis

Tsohon Ministan Buhari Ya Ci Gyaran Shugaba Tinubu a Kan Abubuwa 2 da Ya Aikata a Ofis

  • Raji Babatunde Fashola ya yi magana a kan rigimar mulkin da ake yi a jihohin Ondo da Ribas
  • Tsohon Gwamnan na jihar Legas bai da ra’ayin cewa akwai bukatar sa bakin shugaban kasa
  • Tunde Fashola bai tunanin Bola Tinubu yana da hurumin tsomawa gwamnoni baki a jihohinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Tsohon Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Raji Babatunde Fashola, ya ce ba a bukatar shugaban kasa ya tsoma baki a rikicin siyasa.

Vanguard ta rahoto Raji Babatunde Fashola (SAN) yana bayani ne da fadar shugaban kasa yi kokarin sasanta rigimar mulki a Ondo da Ribas.

Tinubu
Raji Babatunde Fashola da Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Tunde Fashola
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Legas yana ganin babu dalilin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai dinke barakar Gwamna Simi Fubara da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam'iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babutunde Fashola yana da ra’ayin cewa duk da kiraye-kirayen da ake yi na canza tsarin mulki, lokaci ya yi da mutanen kasar za su canza halinsu.

Shugaba Tinubu a rikicin Ondo da Ribas

Lauyan ya ce kundin tsarin mulki ya yi bayani karara a kan abubuwan da ya kamata ayi idan an samu irin rigimar mulkin da ta kaure a Ribas da Ondo.

Kundin tsarin mulkin ya yankewa kowa rawar da zai taka ba tare da katsalandan ba.

An rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi jawabin nan ne a wajen wani taro da kungiyar sojojin sama su ka shirya a garin Legas.

Taken taron wannan shekara shi ne shugabanci da yadda za a kawo sauyi a Najeriya.

Jawabin Fashola a kan Bola Tinubu

"Mun canza tsarin mulki, saboda haka menene ya rage mu canza in bada kan mu?

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun fusata yayin da shugaba Tinubu ya umarci gwamnan PDP ya canza kasafin 2024

Wannan lamarin yana bukatar tsoma bakin shugaban kasa da wasu su ke neman shugaban kasa ya sa baki?
Shin kundin tsarin mulki ya ba shugaban kasa wani rawa da zai taka a lamarin nan?
Ba su ne su ka ce gwamnatin tarayya da shugaban kasa sun yi karfi sosai ba kuma suna shiga hurumin jihohi?

- Babatunde Fashola

Rikicin siyasar Ribas

An ji labari shugaban kasa ba ‘Yan majalisar dokoki umarnin hakura da maganar tsige Simi Fubara daga kujerar Gwamnan jihar Ribas.

Nyesom Wike da ‘Yan Majalisa sun samu yadda su ke so domin za a maido Kwamishinonin da su ka ajiye mukamansu a gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel