Kano: Gawuna Ya Kara Samun Gagarumin Goyon Baya Da Ka Iya Sa Ya Lallasa Abba a Kotun Koli

Kano: Gawuna Ya Kara Samun Gagarumin Goyon Baya Da Ka Iya Sa Ya Lallasa Abba a Kotun Koli

  • Yayin da shari'a kan zaben gwamnan Kano ta kai Kotun Koli, Gawuna na APC ya samu ƙarin goyon baya daga wasu lauyoyi
  • Wata ƙungiyar lauyoyi ta sha alwashin haɗa mambobinta akalla 500 da za su kare ɗan takarar APC a Kotun Kolin Najeriya
  • Kotun sauraron kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara sun tsige Abba, amma ya garzaya kotu mai daraja ta ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Aƙalla lauyoyi 500 masu zaman kansu ne suka nuna sha'awar kare ɗan takarar gwamnan jihar Kano na APC, Nasir Gawuna, a Kotun Kolin Najeriya.

Lauyoyi 500 zasu kare Gawuna a kotun koli.
Kungiya Zata Hada Lauyoyi 500 da Zasu Kare Gawuna a Kotun Koli Hoto: punchng
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne watanni bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da jam'iyyar NNPP sun lashi takobin ɗaukaka ƙara zuwa gaban kotun koli bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin arewa sun bayyana hukuncin da ya kamata kotun koli ta yanke kan zaɓen gwamnoni 3

Idan baku manta ba kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tsige Abba tare da tabbatar da Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen 18 ga watan Maris, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin alƙalan kotun karkashin jagorancin mai shari'a M. A. Adumeh, ya yanke cewa Abba Kabir bai zama cikakken mamban NNPP ba a lokacin da ya tsaya takara.

Lauyoyi 500 zasu kare Gawuna kyauta

Da suke hira da yan jarida a Abuja ranar Talata, tawagar lauyoyin karƙashin ƙungiyar 'Guardians of Democracy and Rule of Law' sun ce sun yanke shawarar haɗa lauyoyi 500.

A cewarsu, zasu tattara waɗannan lauyoyin ne domin ceto demokuraɗiyya daga ƴan aringizon kuri'u da maguɗin zaɓe, masu son yaudarar shari'a.

Mai magana da yawun tawagar lauyoyin, Joseph Onwudiwe, ya shaida wa manema labarai cewa babu wani abu da zai dakatar da su har sai sun tabbatar wa Gawuna da nasararsa a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu shugabannin NNPP sun juya wa Gwamna Abba baya, sun amince da hukuncin kotu

A rahoton The Nation, mai magana da yawun lauyoyin ya ce:

"Muna ƙoƙarin haɗa mambobin mu lauyoyi sama da 500 don kare Gawuna a kotun koli."
"Mun yaba da kuma jajircewa kan gaskiya wanda ta kai ga hukuncin da kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke."

Gwamna Abba da Kwankwaso na tsaka mai wuya

A wani rahoton na daban Rikicin cikin gida a jam'iyyar NNPP ya kara tsanani yayin da tsagin Kwankwaso da Major Abgo suka fara musayar yawu.

A wata hira da yan jarida a Abuja, Major Agbo ya buƙaci jami'an tsaro sun tuhume Kwankwaso kan abubuwaɓ da ke faruwa a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel