Jami'an DSS Sun Kai Samame Fadar Babban Sarki, Sun Kwato Makamai

Jami'an DSS Sun Kai Samame Fadar Babban Sarki, Sun Kwato Makamai

  • Babban basarake a Asaba, Obi Nduka Elunor ya shiga hannun hukumar ƴan sandan fararen kaya (DSS) a jihar Delta
  • An kama basaraken ne bayan jami'an DSS sun kai samame gidansa na tsawon sa’o’i hudu tare da ƙwato muggan bindigogi
  • An tattaro cewa yunƙurin neman belinsa ya ci tura bayan hukumar DSS ta ƙi yarda ta saki basaraken

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Asaba, jihar Delta - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama babban babban basarake a Asaba, Cif Obi Nduka Elunor, bisa zarginsa da laifin yin ƙwacen filaye da kuma mallakar bindigogi ba bisa ƙa'ida ba a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Rahotanni sun nuna cewa yayin wani samame da yammacin ranar Alhamis ɗin da ta gabata a fadar basaraken da ke Anwai, jami'an DSS sun kama wasu mutanen Elunor kusan bakwai yayin da wasu suka yi nasarar tserewa cikin daji.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki a fada, sun yi awon gaba da babban basarake

DSS sun kai samame fadar basarake a Delta
Jami'an DSS sun kwato makamai a fadar basarake a Delta Hoto: DSS
Asali: Twitter

Binciken wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i ana gudanar da shi, ya bankaɗo bindigogi da sauran abubuwan laifi a fadar, rahoton The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka kama basaraken?

Majiyoyi sun bayyana cewa kama Elunor ya samo asali ne daga wani koke da wasu al’ummar yankin suka shigar kan Elunor, inda suka zarge shi da “ƙwatar filaye” a filin Ugwu-Nwosu da ke kusa da Asaba.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, majiyar ya ce:

"Hukumar DSS ta gayyaci Obi Elunor ofishinsu. Yayin da Obi ya je ofishin DSS, jami’an hukumar waɗanda yawansu ya haura 20, suka mamaye fadar Obi."
"An kwato bindigogi ƙirar AK-47 da wasu abubuwa daga fadar, an kama wasu daga cikin mutanensa yayin da wasu suka tsere."
“Hukumar DSS ta ziyarci fadar Asagba kan lamarin, amma Asagba ya ce ba shi ya sanya Obi Elunor ba.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin farmaki kan tawagar ƴan kwallon jihar APC, sun yi musu mummunar illa

DSS ta ki amincewa da bayar da belin basaraken

Haka kuma, wani babban ma’aikacin gwamnatin jihar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa yunƙurin da aka yi na ganin an sako wanda ake zargin bisa beli bai yi nasara ba a lokacin da ya je ofishin DSS a yammacin ranar Juma’a.

A kalamansa:

"A gaskiya ban san komai game da kama shi ba, ina so in ga ko zan iya shiga tsakani. Jami’an sun yi iƙirarin cewa har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin."

Wani babban jami’in DSS, da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma bayyana cewa za a iya bayar da belin Elunor ko kuma a miƙa shi zuwa ga ƴan sanda domin cigaba da bincike.

Yadda DSS Suka Daƙile Juyin Mulki a Lokacin Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa Femi Fani Kayode ya yabi hukumar ƴan sanda fararen kaya (DSS) a ƙarƙashin jagorancin Yusuf Bichi.

A cewar jigon na jam'iyyar APC, a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, hukumar ta daƙile wani yunƙurin juyin mulki da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel